✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bam ya tashi a kusa da filin jirgin sama na Kabul

Ya zuwa wannan lokaci ba a iya tantance irin ta’addin da aka samu ba.

An samu tashin bam a wajen filin tashi da saukar jiragen saman Kabul da ke kasar Afghanistan a yammacin Alhamis.

Ma’aikatar Tsaron Amurka ce ta tabbatar da aukuwar lamarin, sai dai ba ta yi bayanin adadin mutanen da suka ji rauni ko rayukansu suka salwanta ba.

Mai magana da yawun Ma’aikatar Tsaron Amurka, John Kirby ya tabbatar da aukuwar fashewar, sai dai ya ce zuwa wannan lokaci ba a iya tantance irin ta’addin da aka samu ba da kuma yawan mutanen da suka jikkata ba.

Sai a cewar wani jami’an kungiyar Taliban, an samu akalla mutane 11 da tashin bam din ya yi ajalinsu.

Jami’an sun ce cikin wadanda suka mutu har da mata da yara sannan wasu dakarun Taliban sun jikkata.

Bam din ya tashi ne a kofar shiga ta Abbey inda dakarun Birtaniya suke a kwanakin nan.

Kofar na daya daga cikin kofofin da aka rufe bayan gargadin da aka yi ta yi na barazanar ta’addanci.

Wani jami’in Amurka ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters cewa wani dan kunar bakin wake ne ya tayar da bam din.

Fadar White House ta tabbatar da cewa an sanar da Shugaba Biden halin da ake ciki.

Wannan lamari dai ya girgiza birnin sa’o’i bayan kasashen yammacin duniya sun yi gargadi samun kai harin ta’addanci a filin jirgin da ke dauke da dubban mutanen da ke kokarin tserewa daga kasar.

Jami’an kasashen yamma sun umarci dandazon mutanen da suka taru a kofofin shiga filin jirgin da su bar wajen saboda ana zaton za a iya kai harin ta’addanci.

Bayanai sun ce ya zuwa yanzu akalla mutane dubu 95 daga cikin ‘Yan kasashen waje da ‘Yan kasar Afghanistan suka yi nasarar barin Afghanistan tun bayan fara jigilar su ranar 15 ga watan Agusta sakamakon karbe iko da kasar da kungiyar Taliban ta yi.