✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Bam ya kashe mutum 8 a wajen ofishin jakadancin Rasha da ke Afghanistan

Bam din ya tashi ne lokacin da mutane ke layin neman biza

Akalla mutum takwas sun mutu bayan wani dan kunar-bakin-wake ya tayar da bam a kusa da kofar ofishin jakadancin Rasha da ke birnin Kabul na Afghanistan.

Wasu majiyoyi a jami’an tsaron kasar sun shaida wa gidan talabijin na Aljazeera cewa daga cikin mutanen da suka mutu har da wasu ma’aikatan ofishin su biyu.

Ma’aikatar Harkokin Wajen Rasha ta wallafa a shafinta na Twitter cewa, “A sakamakon harin, an kashe ma’aikatan ofishin su biyu, sannan akwai ’yan Afghanistan da harin ya shafa.”

Sai dai ma’aikatar ba ta yi karin bayani ba a kan su waye ma’aikatan da kuma yadda suka mutu.

Tun da farko dai, kamfanin dillancin labaran Rasha na RIA Novosti ya ambato wasu majiyoyi da aka sakaya sunansu cewa akalla mutum 15 zuwa 20 ne suka rasu ko suka jikkata a harin.

Majiyoyin sun ce an kai harin ne a daidai lokacin da mutane ke tsaye a kan layi suna so a kira su domin samun bizar shiga kasar.

Wani dan jarida da ke birnin na Kabula, Najib Lalzoy, ya shaida wa Aljazeera cewa, “Fashewar bam din ta auku ne a wajen ofishin jakadancin inda mutane ke bin layi domin samun bizar shiga Rasha.”

Mazauna yankin sun ce akwai cincirindon mutane a wajen lokacin da bam din ya tashi wajen maisalin karfe 10:50 na safiyar Litinin a agogon kasar.