Akalla mutum 13 ne suka mutu sannan wasu mutum uku suka ji rauni bayan da wasu bama-bamai biyu suka fashe a Damascus, babban birnin kasar Siriya.
Kamfanin Dillacin Labaran Kasar Siriya (SANA) ne ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Laraba.
- Allah ya yi wa babbar jikar Sardauna rasuwa
- Daga Laraba: Neman mafita daga matsalar watsi da tarbiyyar ’ya’ya (2)
A cewarsa, ’yan ta’adda ne suka binne bam din a karkashin kasa inda wata mota ta taka yayin da take tsallake wata gada da ke birnin na Damascus.
Kafafen watsa labarai, musamman talabijin sun nuna yadda motar ta yi kaca-kaca bayan taka bam din.
SANA, ya rawaito cewar jami’an tsaro sun yi nasarar cire bam na uku da aka dasa a yankin.
A halin da ake ciki, kungiyar da ke sa ido kan kare hakkin bil adama a Siriya da ke Birtaniya, ta ce fashewar ta kashe mutum 14 kuma akwai yuwuwar adadin ya karu.
Masu sa ido da SANA duk sun ce bas din na dauke da sojojin Siriya lokacin da ta taka bam din.