Wani abin fashewa ya tashi a wani masallaci da ke yankin Spin Ghar a gabashin Afghanistan ana tsaka da Sallar Juma’a, inda ya kashe mutane da dama kuma raunata mutum 15.
Wani jami’in Taliban da ba a bayyana sunansa ba ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na AFP cewa fashewar ta haddasa mutuwa da kuma ji wa mutane rauni.
- Jiragen yaki sun hallaka shanu 1,500 a kauyukan Fulani
- Yadda kasa ta binne matasan Najeriya 13 a rijiyar hakar zinare a Nijar
“Na tabbatar an samu fashewa yayin Sallar Juma’a a cikin masallacin gundumar Spin Ghar,” a cewar jami’in.
Mai magana da yawun gwamnati a yankin, Qari Hanif, ya fada wa Kamfanin Labarai na AFP cewa da alama a cikin masallacin aka dasa bam din.
Walli Mohammed, wani dattijo kuma dan gwagwarmaya a yankin, ya shaida wa AFP cewa an boye bam din ne a cikin lasifikar masallacin wanda ya tashi bayan an kunnata domin yin kiran sallah.
Ya zuwa yanzu babu kungiyar da ta dauki alhakin kai harin amma kungiyar ISKP wani reshe na kungiyar ISIS ta sha kai hare-haren bam tun bayan da Taliban ta kwace mulkin kasar.
Makonni biyu da suka gabata ne kimanin mutum 25 suka mutu sannan gommai suka jikkata, sakamakon wani hari da aka kai asibitin sojoji da ke Kabul, babban birnin kasar Afghanistan.
An fara kai harin ne a lokacin da wani dan kunar bakin wake ya tayar da bam a kusa da kofar shiga asibitin Sardar Daud Khan, inda daga bisani wasu dauke da bindigogi suka shiga harabar asibitin tare da yin harbi kan mai uwa da wabi.