✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Bam ya kashe masu ibada da dama a coci a Jihar Ondo

Maharan sun kuma bude wuta bayan tashin bam din

Mutane da dama ne ake fargabar sun mutu bayan wani bam ya tashi a Cocin Katolika ta St. Francis da ke Owa-luwa a yankin Karamar Hukumar Owo ta Jihar Ondo, lokacin da suke tsaka da ibada.

Har yanzu dai babu cikakkun bayanai kan harin har zuwa lokacin hada wannan rahoton, amma wata majiya a kusa da inda lamarin ya faru da harin ’yan ta’adda.

Kazalika, majiyar ta ce maharan sun kuma bude wuta a kan masu ibada bayan tashin bam din.

Cocin dai na kusa da Fadar basaraken Owo, wato Olowo na Owo.

Owo dai nan ce mahaifar Gwamnan Jihar ta Ondo, Rotimi Akeedolu.

Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar, Funmilayo Odunlami, ta tabbatar da faruwar lamarin, amma ta ce yanzu haka suna ci gaba da bincike a kai.