✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Bam ya halaka babban mai kera wa Boko Haram bama-bamai a Borno 

Ya mutu ne lokacin da yake hada wa kungiyar bam

Babban mai kera wa kungiyar Boko Haram bama-bamai, Awana Gaidam, ya mutu bayan fashewar naurar da ya saba hada wa kungiyar a lokacin da yake kokarin amfani da ita don hada bam din.

Majiyoyin soja sun bayyana hakan a matsayin wani babban ci gaba a aikin rundunar da suke yi a yankin Arewa maso Gabas.

Babban mai kera bama-baman mai shekara 39, Awana Geidam, baya ga irin matsayin da yake da shi a cikin kwamandojin ’yan ta’addan na Boko Haram, yana kuma daya daga cikin masu iya kokarinsu wajen kera abubuwan fashewa da ke halaka jama’a.

Wannan na nuna  cewa, Boko Haram ta yi matukar samun koma-baya a fada da suke da bangaren ISWAP da kuma bangaren dakarun sojan Najeriya da dakarun MNJTF da ke yankin Tafkin Chadi.

Majiyar Zagazola Makama, kwararre kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi na kyautata zaton cewar, Awana shi ne ke da alhakin shirya hare-haren bama-bamai da dama a kan sojojin Operation Hadin Kai a lokacin da suke sintiri, a kan manyan hanyoyin da ke tsakanin Maiduguri zuwa Damboa, Bama zuwa Pulka da Bita da kuma yankin Banki zuwa Darajamal.

Majiyoyin leken asiri sun bayyana cewa bam din ya tarwatsa motarsa a Njumia da Arra a cikin dajin Sambisa, a ranar 27 ga watan Maris, inda nan take ya mutu.

Majiyar ta bayyana cewa Awana ya dasa bama-baman ne a wurare masu mahimmanci domin bada tsaro a sansaninsa da ke cikin dajin sambisa amma bai sani ba ya shirya hakan ne a kan kansa, lamarin da ya sa ya fasa shi ya yi kaca-kaca gawarsa.

Tun daga shekarar 2022, kungiyar Boko Haram da Daular Islama ta yammacin Afirka (ISWAP) suka kai hare-hare sama da 90 a yankin Arewa maso Gabas ta hanyar amfani da na’urori masu fashewa (IED).

’Yan ta’addan sukan  yi amfani da bama-bamai ne sakamakon karuwar da kuma ci gaba da matsin lamba daga hadin gwiwar sojojin Najeriya, rundunar sojojin sama, Operation Hadin Kai tare da goyon bayan rundunar hadin gwiwa ta Multination Joint Task Force (MNJTF), Nijar Kamaru da Chadi.

Mutuwar Awana, karara na nuna babban tsaiko ga ikon gudanar da ayyukan kungiyar Jama’at Ahl as-Sunnah lid-Da’wah wa’l-Jihād, Boko Haram .