✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bala Mohammed ya kafa kwamitin binciken zaluncin ‘yan sanda

Gwamnan jihar Bauchi Bala Mohammed, ya kafa kwamitin binciken zaluncin jami’an ‘yan sanda na SARS a jihar. Gwamna Bala ya kafa kwamitin ne a ranar…

Gwamnan jihar Bauchi Bala Mohammed, ya kafa kwamitin binciken zaluncin jami’an ‘yan sanda na SARS a jihar.

Gwamna Bala ya kafa kwamitin ne a ranar Laraba domin bincikar laifukan ‘yan sanda a jihar biyo bayan korafe-korafe da jama’ar jihar suka shigar gaban gwamnatin jihar, bisa laifukan da suka shafi zalunci da cin zarafin al’umma.

Gwamnan ya bawa kwamitin tsawon watanni shida ya gudanar da binciken tare da gabatar masa da sakamako domin daukar matakin shari’a da ya dace.

Kwamitin karkashin jagorancin tsohon Mai Shari’a Habibu idris a matsayin shugaba, sai tsohon Shubagan Hukumar ‘Yan Sandan jihar CP Hamisu Makama da kuma sauran masu ruwa da tsaki a jihar daga kungiyoyi masu zaman kansu a matsayin mambobi.

Ana sa ran kwamitin zai fara gudanar da aikinsa daga mako mai zuwa domin samar da sakamakon bincikensa a kan lokaci.