Karin mutum uku sun mutu ta dalilin bullar wata bakuwar cuta a Epeilo-Otukpa, Karamar Hukumar Ogbadibo ta Jihar Binuwai.
Mutum 20 ke nan suka mutu sakamakon bakuwar cutar wadda Ma’aikatar Lafiyar jihar ta sanar da bullarta ranar Talata.
- Tsadar fetur ta sa Buhari komawa motoci masu aiki da gas
- Babu kotu ko caji ofis din da aka kai ni —Rahama Sadau
“Ma’aikatar na aiki a yankin, ta kai marasa lafiyan asibitoci ta kuma kai samfurin jinsu babban dakin gwajin cutuka na kasa domin a binciko kwayar cutar da ke haddasa rashin lafiyar”, inji ma’aikatar.
Babban Masanin Cututtuka na jihar, Dokta Sama Ngishe ya ce cikin mutum ukun da cutar ta kashe har da shugaban matasan unuguwar.
Dokta Ngishe ya ce cutar ta kashe maza 19 da mace daya daga cikin mutum 26 da suka nuna alamunta wadanda shekarunsu bakwai zuwa 66 ne.
Ya ce, “Muna zargin cutar na da alaka da shawara duba da bullarta a jihohin Edo, Enugu da Delta, amma ba a saba ganin bullarta ta wannan yanayi ba.
“Yanzu gwamanin jihar na shirin fara wayar da kai kan cutar tare da kula da marasa lafiyar domin takaita yaduwarta da illar za ta iya yi.
“Matsalar ita ce al’ummar yankin ba su yi saurin sanarwa ba saboda sun dauka mutanen da suka aikata sabo ne abin ke shafa”, inji shi.
Dokta Ngishe ya ce an kwantar da mutum biyu a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jihar Binuwai a dalilin bakuwar cutar.
Ya ce wasu masu cutar sun ki yarda a kai su manyan asibitoci, wadanda nasu bai yi tsanani ba kuma suna Asibitin Tarayya da ke Efeko da kuma Babban Asibitin Otukpa.