Akalla mutane 17 ne suka mutu sakamakon barkewar wata bakuwar cuta a karamar hukumar Okpeilo-Ogbadibo dake jihar Benuwe.
Hakan na dauke ne cikin wata sanarwa da sakataren hukumar lafiyar jihar Sir Andrew Amee ya fitar a madadin Kwamishinan lafiyar jihar a ranar Talata.
- An yi garkuwa da likitoci biyu da ma’aikacin asibiti a Benuwe
- An gano gawarwaki 30 da aka birne a Benuwe
- Mutuwar mutum 35 ta sa za a fara rigakafin cutar shawara a Delta
- ‘A guji sayen ruwan leda don kauce wa cutar AIDS’
“Mun samu rahoton bullar wata cuta da bamu gano kanta ba a karamar hukumar Okpeilo-Ogbadibo”.
“A ranar 9 ga watan Nuwamba mun samu rahoton mutuwar mutane 17 a sakamakon harbuwa da suka yi da cutar”.
“Yanzu haka muna da wanda ya kamu da cutar a asibitin koyarwa na jami’ar Benuwe inda ake kula da shi, ragowar kuma suna asibitoci daban-daban na jihar nan”, inji Amee.
Ya kara da cewa alamomin cutar sun hada da zazzabi, kasala, amai, gudawa, ciwon jiki da sauransu.
Har wa yau, Amee ya kara da cewa gwamnan jihar Samuel Ortom ya ware kudi ga hukumar lafiya ta jihar, domin gudanar da bincike tare da gano musabbabin bullar cutar.
Sannan ya ja hankalin jama’ar jihar da su kasance masu tsaftace muhallinsu domin guje wa kamu wa da cututtuka barkatai.