✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bakon saurayi

Wani Bakatsine ne ya je wurin budurwarsa, suna cikin hira sai kawai hadari ya taso. Kafin ka ce me, an fara ruwan sama mai karfin…

Wani Bakatsine ne ya je wurin budurwarsa, suna cikin hira sai kawai hadari ya taso. Kafin ka ce me, an fara ruwan sama mai karfin gaske. Ganin haka sai baban yarinyar ya fito daga gida ya ce mata: “Da alamu wannan ruwan ba mai tsagaitawa ba ne, watakila a kwana ana yi, ki shiga ki gyara mai dakin baki; da safe sai ya tafi.” Nan da nan ta shiga gida ta fara gyara daki. Tana gamawa sai suka fito, ba su ga Bakatsine ba. Can sai ga shi nan ya shigo a guje, duk ya jike jagaf. Baban yarinyar ya tambaye shi cewa daga ina ya fito haka, sai saurayin ya ce: “Gidanmu na je na dauko bargona saboda na san za a yi sanyi cikin dare.”

Daga Nura Suleja, 08107575716