Bello Matawalle na Jihar Zamfara ya zargi cewa ’yan kasashen waje da na sayen zinare da sauran ma’adinai masu daraja su bayar da makamai a jiharsa.
Ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin amsa tambayoyin ’yan jarida bayan ya gabatar da zinarai da wasu duwatsu masu daraja ga shugaba Muhammadu Buhari a fadarsa da ke Abuja.
Ya ce, “A matsayinmu na gwamnati ya kamata mu gano matsalar tsaron da ta addabe mu daga tushe. Allah Ya albarkaci Jihar Zamfara da ma’adinai da dama.
“Wasu mutane na zuwa daga kasashen ketare domin sayen wadannan ma’adinan, amma maimakon su biya da kudi sai su rika bayar da makamai.
“Na yi bincike kafin gano hakan, kuma gwamnatin jiharmu ta yanke shawarar sayen ma’adinan da kanta in ya so ta saysar wa da ’yan kasashen wajen ta hannunta domin a yi wa tufkar hanci.
“Za mu rika saye daga hannun masu hakowa kai tsaye mu kuma mu je mu sayar”, inji gwamnan.
Matawalle ya ce gwamnatinsa ta yanke shawarar rungumar sabon tsarin hakar ma’adinan na Fadar Shugaban Kasa domin kawo karshen badakalar cinikinsu a jihar.
– Sauya Hafsoshin Tsaro ba shi ne mafiya ba
Game da kalubalen tsaron da ya addabi jiharsa kuwa, Matawalle ya ce sannu a hankali ana samun sassauci.
Ya kuma kalubalanci masu kira a sauke manyan hafsoshin tsaron kasa, yana mai cewa abin da suka fi bukata a yanzu shi ne karin hadin kai da kwarin gwiwa daga dukkannin masu ruwa da tsaki.
“Yanzu labari ya canza a jihata. An daina jin labarin kisan mutane da yawa kamar a baya saboda jami’an tsaro a jihar sun kara daura damara.
“Na kuma ba wa Shugaban Kasa shawara cewa cire Manyan Hafsoshin Tsaro ba shi ne maslaha ba. Kamata ya yi a kara karfafa musu gwiwa. Mu a matsayin mu na gwamnoni muna da muhimmiyar rawar da za mu taka a kan haka.
“Idan gwamnoni ba su yi da gaske ba, babu yadda za a yi hakarsu ta kai ga cimma ruwa. Idan ma cire Manyan Hafsoshin Tsaron ai wasu dai za ka kawo.
“Kamata ya yi kawai mu ci gaba da lallabawa da wadanda muke da su. Za mu taimaka musu a matsayinmu na gwamnati
“Yanzu haka jihata ta samu zaman lafiya, kuma kowa shaida ne a kan hakan.
“Mun jibge jami’an ’yan sanda kusan 3,000 da ke sintiri a wuraren hakar ma’adinan domin kare su.
“Muna da jami’an tsaro, abin da kawai ya kamata mu yi a matsayinmu na shugabanni shi ne mu karfafa musu gwiwa. Ina da kyakkyawan zaton cewa nan ba da jimawa ba za a samu ingantuwar tsaro a kasar nan”, inji gwamna Matawalle.