Hukumar Kula da Masu Hijira ta Duniya (IOM) ta ce akalla bakin haure 50,000 ne suka mutu a fadin duniya.
Hukumar ta ce bakin hauren sun mutu ne bayan jefa rayuwarsu cikin hadarin yin kaura zuwa kasashen waje don samun ingantacciyar rayuwa.
- NAJERIYA A YAU: Rikicin PDP: Shin Atiku zai kai bantensa a 2023?
- A Najeriya aka buga sabbin takardun kudi —Buhari
“Yayin da akan samu dubban bakin hauren da ke mutuwa a hanya duk shekara, babu wani kokarin kirki da aka yi don shawo kan matsalar balle hana aukuwarta,”inji hukumar.
IOM ta bayyana a cikin wani sabon rahotonta da ta fitar ranar Laraba, cewa wannan adadi na wadanda suka mutu ne tun daga 2014.
Rahoton hukumar ya nuna babu wani kokarin a-zo-a-gani da kasashe ke yi don kula da lamarin bakin haure a yankunansu.