✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Bakin Balarabe: Bakatsinen da ya je Babban Taron APC na Abuja a kan rakumi

Ya ce ya yi tafiyar ce don ya nuna tsantsar soyayyar da yake yi wa APC

A ranar Asabar din da ta gabata ce jam’iyyar APC mai mulki ta gudanar da Babban Taronta na kasa a dandalin Eagle Square da ke Babban Birnin Tarayya Abuja.

Baya ga ainihin taron, abubuwa da dama sun taru daga gefe, wadanda suka ja hankulan mutane, wasu ma ba a san sun faru ba.

Alal misali, akwai wani Bakatsine mai suna Ibrahim Yahaya Hamisu, wanda aka fi sani da Bakin Balarabe, ya shafe kilomita 590 wajen yin tafiya tun daga Katsina har zuwa Abuja don halartar taron a kan rakumi.

Mutumin dai ya shafe kimanin sa’a 120 (kusan kwana biyar) a kan hanyar tasa kafin ya isa, duk kuwa da kalubalen tsaron da ake fama da shi a hanyoyin da ya bi.

Bakin Balarabe ya ce ya yi tafiyar ne don ya nuna wa ’yan Najeriya irin son da yake yi wa APC

Jaridar Vanguard ta rawaito cewa da aka tambaye shi makasudin yin tafiyar, sai ya ce, “Na yi ne saboda sun da nake yi wa APC.”

Ya ce a yayin tafiyar tasa dai, mutane a garuruwan da ya wuce sun rika tsayar da shi suna tattaunawa da shi tare da daukar hotuna tare da shi, inda ya ce sune ma suka dada karfafa masa gwiwa.

“Yayin da nake tafiyar, mutane da dama, ciki har da masu motoci sun rika tsayawa suna yi min tambayoyi, wasu ma har hoto suke tambayata mu dauka,” inji shi.

Sai dai Bakin Balarabe ya ce tilas ta sa ya kashe wayoyinsa iya tsawon kwanakin tafiyar saboda dalilan tsaro da ma wasu dalilan na kashin kansa.