✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bakar magana

Wasu mutane ne su uku suna zaune sai ga mai sayar da nama zai wuce. Suka kira shi domin su saya, daya ya ce a…

Wasu mutane ne su uku suna zaune sai ga mai sayar da nama zai wuce. Suka kira shi domin su saya, daya ya ce a yanka masa na Naira hamsin, shi ma dayan ya ce a yanka masa na hamsin. Sai aka tambayi dayan shi kuma na nawa za a yanka masa, sai ya ce: “Ni likita ya hana ni cin nama amma dai dan yanko mani kadan in dandana.” Mai nama ya yanka masa, ya saka a baki ya ji dadi, sai ya ce masa: “Yanko mani na Naira ashirin.” Jin haka sai mai nama ya ce: “dauko baro!”

Daga Aminu M. Ibrahim, 09034793420