Wani Bakanon da ya fara tattaki daga Abuja zuwa Legas domin nuna goyon bayansa ga takarar Bola Tinubu, Husseini Lawal, ya isa Ibadan babban birnin Jihar Oyo.
Mutumin dan asalin Jihar Kano ya fara tattaki ne zuwa Legas tun bayan da Tinubu wanda jigo ne a jam’iyar APC mai mulki ya bayyana kudurinsa na tsayawa takarar shugabancin kasar nan a kakar zabe mai zuwa.
- Harin jirgin kasa: Har yanzu muna cigiyar mutane da dama – Gwamnatin Kaduna
- Real Madrid ta kora PSG gida; Man City ta tsallaka zagaye na gaba
Hussein ya isa birnin Ibadan a daren Litinin inda ya bayyana cewa yayin tattakin nasa yana samun tallafi na kudi da sauran abubuwa daga sojoji da direbobin da yake haduwa da su a kan hanyarsa.
Har ila yau, ya shaida wa wakilinmu cewa ya fara tattakin ne domin nuna cikakken goyon bayansa ga tsohon Gwamnan na Legas saboda ya ce shi kadai ne dan takarar da ya damu da matasa a cikin masu neman takarar a 2023.
“Tinubu ya goyi bayan matasa tun kafin ya zama Gwamna a Legas; haka kuma lokacin da yake Gwamnan da ma bayan ya bar kujerar,” inji mai tattakin.
Daga karshe ya yi kira ga ’yan Najeriya da su mara wa Tinubun baya a zabe mai zuwa.