Shugaban Hukumar Shirya Jarabawa ta Kasa (NECO), Farfesa Ibrahim Dantani Wushishi ya yi kira da a daina amfani da tsarin tilasta samun sakamako a darussan Turanci da Lissafi kafin samun gurbin karatu a manyan makarantun Najeriya.
Ya bayyana haka ne yayin da yake jawabi a taron Kungiyar Makarantun Islamiyyah a Minna, babban birnin Jihar Neja ranar Asabar.
- Rashin tsaro: Alarammomi da CNG sun fara addu’,o’i na musamman
- An kama ma’aurata sun shirya wa jaririn da suka sace biki
Ya kuma yi kira da a kafa kotu ta musamman don hukunta masu magudin jarrabawa domin a cire tarnakin da ake fuskanta wajen gurfanarwa da kuma hukunta masu aikata laifin satar jarabawar.
Farfesa Wushishi, a cikin makalar da ya gabatar mai taken: “Yadda za a magance magudin jarrabawa domin ci gaban kasa”, ya ce, “Ya kamata Gwamnatin Tarayya ta rage yawan tasirin da take ba takardu a kan komai a kasar nan, wajen tantancewa da kuma ba da sakamako ga dalibai da ma’aikata.”
Shugaban na NECO ya lura cewa tsare-tsare da manufofin gwamnati a kan harkar ilimi na bukatar garanbawul, inda ya ce akwai bukatar samar da isassun kayan aiki a makarantun gwamnati don inganta harkar koyo da koyarwa.
A cewarsa, Jihohin da aka fi samun matsalar magudin jarrabawa sun hada da Bauchi da Borno da Kano da Kebbi, musamman a cikin shekaru biyar da suka gabata.
Sai dai ya zargi iyaye da malamai da ma tsarin gudanar da makamantun a matsayin ummul’aba’isun tabarbarewar al’amura.
Ya ce ya zama wajibi a hada karfi da karfe wajen magance matsalar ilimi a Najeriya.