Shugaban kungiyar Dillalan Motoci ta kasa reshen Jihar Filato kuma Shugaban Kamfanin Sayar da Motoci na Kega Motors da ke garin Jos, Alhaji Yahaya Muhammad Kega, ya ce bai kamata ’yan kabilar Ibo su goyi bayan a raba Najeriya ba.
Alhaji Yahaya Muhammad Kega ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da Aminiya kan rikicin da ya faru mako biyu da suka gabata, inda masu fafutikar neman kafa kasar Biyafara suka kai wa ’yan Arewa da ke yankin Ibo hare-hare, wanda ya yi sanadin fara daukar fansa a garin Jos.
Ya ce wannan rikici wani abu ne marar dadi kuma na rashin kan gado. Domin ainihin wadanda suke tayar da rikicin ba su zaune a Najeriya, musamman shugaban tafiyar, Nnamdi Kanu.
Alhaji Kega ya ce ya kamata ’yan kabilar Ibo su fahimci cewa ’yan Arewa sun karbe su hannu bibbiyu shekara da shekaru, sun ba su masauki sun ba su komai na karramawa. Ya ce idan aka ci gaba da wannan rikici Ibo ne za su cutu kuma su ne za su yi asara.
Alhaji Yahaya Kega ya ce idan aka kasa yawan arzikin Arewa gida uku, kashi daya na Ibo ne. Kuma duk wasu harkokin kasuwanci da za a yi a Najeriya, dole sai an hada da Ibo. Don haka idan da tunani mai dukiya ba zai so a yi fada ba.
Ya ce, “Illolin da rikici zai kawo wa Ibo suna da yawa. Na farko za su yi asarar abubuwan da suka mallaka, kuma nan gaba babu wanda zai saki jiki ya sake hulda da su. Don haka ina kira ga al’ummar Ibo da sauran al’ummar Najeriya su yi hakuri da juna su zauna lafiya domin a ci gaba da samun zaman lafiya da kwanciyar hankali.