✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bai kamata a samu sabani tsakanin Ganduje da Kwankwaso ba

Ba abin mamaki ba ne ganin yadda rikicin siyasa take ruruwa tsakanin tsohon Gwanman Kano Dokta Rabiu Musa Kwankwaso da magajinsa, Dokta Abdullahi Ganduje, domin…

Ba abin mamaki ba ne ganin yadda rikicin siyasa take ruruwa tsakanin tsohon Gwanman Kano Dokta Rabiu Musa Kwankwaso da magajinsa, Dokta Abdullahi Ganduje, domin kuwa an dade ana rade-radin cewa akwai sabani a tsakaninsu.
Masoya da makusantan tsohon  Gwamnan suna tuhumar sabon gwamnan da sanya tsohon gwanman a cikin Kwandon shara, ta hanyar yin watsi da shawarwarinsa a yayin nada  kwamishinoni da sauran mukamai masu mahimmanci, kuma sun zarge shi da kokarin nuna cewa wadansu daga cikin tsare-tsaren tsohon gwanman ba su da muhimmanci ga mutane, inda ya yi musu gyaran fuska ko kuma ya canja su baki daya. Kuma uwa uba ya yi kokarin dauko wadansu ayyuka na tsohon Gwamna Ibrahim Shekarau, wadanda Kwankwaso ya yi watsi da su.
 A dayan bangaren kuma su magoya bayan Ganduje suna ganin cewa, yanzu zamaninsu ne kuma ba a sarki biyu, don haka suna ganin ba sa bukatar takura da sa ido daga tsohon gwamnan. Wannan ba abin mamaki ba ne, musamman ga mutanen Kano, domin kuwa da yawa daga cikin mutanen sun dade suna sauraron zuwan wannan lokacin, ganin yadda magoya bayan tsohon gwamnan da na sabon gwamnan suke sukar junansu a kafafen yada labarai, kamar gidajen rediyo da yanar-gizo irin su facebook da twitter da makamantansu.
Babbar alamar da ta nuna cewa za a samu matsala, ita ce, yadda magoya bayan Kwankwaso suka taru a filin jirgin sama na Aminu Kano domin tarbarsa yayin da ya je yin ta’aziyya ga Gwamna Ganduje domin rashin da ya yi na mahaifiyarsa.
A ganina wannan hatsaniyar ba kawai rikici ne tsakanin Kwankwaso da Ganduje ba, magana ce ta rainin hankali da cin amana. Domin kuwa shekara daya ta yi kadan a warware abota da kuma amincin da aka kulla na shekaru da yawa, idan dai har wannan abotar an kulla ta ne kan gaskiya da amana.
Tarihi ya nuna cewa, Kwankawso da Ganduje sun dade tare, domin kuwa ko bayan da Kwankwaso ya zabi Ganduje a matsayin mataimakinsa a shekarar 1999, ya fada cewa ya zabe shi ne domin sun dade tare. Sannan a shekarar 2007 a maimakon Gaduje ya goya wa mai gidansa baya domin a gudu tare a tsira tare, sai shi ma ya tsaya takarar gwamna da niyyar canja maigidansa, wato Kwankwaso. Allah cikin ikonSa sai  Kwankwaso ya yi nasarar doke Ganduje da sauran takwarorinsa, wadanda suka yi takara a waccan shekarar ta 2007. A wannan lokacin Ganduje ya jagoranci wadansu daga cikin takwarorinsa su biyar wurin nuna rashin amincewarsu da nasarar Kwankwaso. Duk da haka bai hana Kwankwaso ya cigaba da tafiya tare da shi ba. Cikin ikon Allah sai suka sha kaye a hannun Malam Ibrahim Shekarau na Jami’iyar ANPP.
Bayan an gama juyayin shan kaye ne kuma sai shugaban kasa a wancan lokacin, wato Cif Olusegun Obasanjo ya nada Rabi’u Kwankwaso a matsayin ministan tsaro. A nan ma Kwankwaso sai ya tafi tare da Ganduje. Kuma a shekarar 2011 lokacin da aka sake zabe, Kwankwaso ya kara dawowa tare da Ganduje, bayan mutanen Kano sun bukaci dawowarsa kan kujerar Gwamnan Kano, kamar yadda Nazifi Asnanic ya nuna a cikin shaharrariyar wakarsa ta ‘’Kwankwkaso dawo.’’ Kuma cikin ikon Allah sai suka yi nasara.
Sannan a shekarar 2015, duk da nuna rashin amincewar mafi yawa daga cikin kwamishinoni da masu  fada-a-ji na jami’iyyar APC ta Kano a wannan lokacin, Kwankwaso ya shiga, ya fita, har sai da ya tabbatar Ganduje ya samu karbuwa da kuma nasarar lashe zaben shekarar domin zama sabon Gwmanan jihar Kano.
Bayan haka, domin ya bar sabon gwanman ya natsa, ya samu damar dorawa daga inda aka tsaya, sai da Kwankwaso ya dauki watanni kusan tara bai je garin Kano ba, har sai da mahaifiyar shi sabon gwamanar ta rasu, wanda ya zame masa dole ya je, ganin yadda suka dade suna fadi-tashi tare.
Amma saboda kyashin soyayyar da mutane suka nuna wa Kwankawaso yayin da suka tarbe shi, sai aka tursasa shugaban jam’iyyar APC na Jihar Kano ya fito ya bayyana cewa wai za a ladabtar da Kwankwaso, domin ya tayar wa mutane da hankali. Sai dai daga baya shugaban jam’iyyar ya fito ya fada wa duniya cewa, shi ya janye wannan maganar, domin dama tun farko an tursasa shi ne ya fada.
A karshe, ina ganin mutum kamar Kwankwaso, wanda ya taimaki mutane da yawa ta hanyar daukar nauyin karatunsu a gida da waje da ba su ayyukan yi da dai sauransu, ba zai yiwu ba ka raba shi da mutane, domin wadannan mutanen za su iya mutuwa saboda shi, sannan  kuma a kodayaushe suka ganshi dole ne su karbe shi da hannu bibbiyu. Domin haka ya kamata shi ma sabon gwamnan Kano ya yi abubuwan da za su amfani rayuwar mutanen Kano, ya gina su kamar yadda Kwankwason ya gina su, sai shi ma a so shi kamar yadda ake son Kwankwaso. Amma idan ba haka ba, zai kara wa kansa bakin jini ne a wurin mutane, domin masu iya magana suna cewa fada da aljani ba riba.
Daga: Isiyaku Muhammed, Hayin Banki, Kawo, Kaduna, 07036223691.