✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bai kamata a manta da matsalar tsaro ba – danmalikin Argungun

Aminiya: Ka gabatar mana da kanka?danmaliki: Sunana Alhaji Musa Abubakar danmalikin Argungu, Ma’ajin Jam’iyyar APC na Jihar Kebbi, kuma tsohon ko’odinetan kungiyar goyon bayan Buhari,…

Aminiya: Ka gabatar mana da kanka?
danmaliki: Sunana Alhaji Musa Abubakar danmalikin Argungu, Ma’ajin Jam’iyyar APC na Jihar Kebbi, kuma tsohon ko’odinetan kungiyar goyon bayan Buhari, wato Buhari Support Organisation a jihar Kebbi.

Aminiya: Jam’iyyarku ta samu nasarar kafa gwamnati a Jihar Kebbi kwatsam sai ga shi wasu daga cikinku shugabannin jihar a jam’iyyar na neman shugaban ku Alhaji Attahiru Maccido da ya sauka daga kan mukaminsa. Me za ka ce a kan wannan?
danmaliki: Dalilai da dama ne suka kai ga hakan, duk a sakamakon yadda yake gudanar da shugabancinsa. Shi dai shugaba ne, amma a kwai mataimaka da a ka zabe su tare da shi don su tafiyar da sha’anin jam’iyyar tare da shi, kamar ni ma’aji, da sakataren kudi, da odita da dai sauransu, wadanda a ka’ida idan al’amari na jam’iyya ya tashi kamata ya yi ya kira taro, a yi zama, ya kawo shawara ba zartar da al’amari shi kadai ba, ciki har da sha’anin  sarrafa kudin jam’iyya, wanda a tsari shi ne idan mambobin kwamitin gudanarwa ta jam’iyya ta amince da yin wani abu, dole ne sai an samu sa hannun mutum uku da suka hada da shi kansa, da sakataren kudi, da ni ma’ajin jam’iyya kafin a fitar da kudi.
Sannan ga cike gurabun shugabanci a duk lokacin da a ka rasa wani ta hanyar rashi ko dakatarwa, ba tare da bin yadda ka’idar jam’iyya ta tsara ba. Ganin yawaitar hakan ni da sakataren kudi, wanda hakkin jama’a ke kanmu mun je banki don sanin abin da a ke ciki, amma banki sun daure masa gindi sun ki ba mu bayani. A kwai kuma matsalar rashin kiran taron uwar jam’iyya, kamar yadda tanadin ya nuna daga lokaci zuwa lokaci.  

Aminiya: To wane koma baya kuke jin hakan ya jawo wa jam’iyyarku?
danmaliki: korafe korafe na rashin matsayi da ake ciki game da kudin jam’iyya, ciki har da kudi  da aka tara wajen sayar da fom na tsaya wa takara da muka tattara, muka bai wa uwar jam’iyya a Abuja. Kowacce jiha ta amfana da wani kaso daga cikin abin da ta kai, wanda uwar jam’iyya ta ba ta, don gudanar da ayyukanta a matakin jiha da kananan hukumomi, kamar yadda takororimu da ke rike da mukamanmu a wasu jihohi suka tabbatar mana. To, amma mu a Jihar Kebbi bayanin da yake yi mana, shi ne, ba a ba da kudin ba duk da tabbacin da muke da shi na an bayar, kamar yadda na shaida maka.
Aminiya: A ka’ida idan a ka samu irin wadannan korafe-korafe a kan kai kuka ga uwar jam’iyya ta kasa, ko kun dauki irin wannan mataki.
danmaliki: Hakika mun sanar da su,  kuma mun fara ne daga mataki na yanki, wanda ya kunshi jihohi  bakwai na Arewa maso Yamma da Barista Inuwa Abdulkadir ke shugabanta, bayan wata uku ba tare da wani mataki ba, sai muka kai korafi ga uwar jam’iyya ta kasa da ke nan Abuja.
Sannan muka dauki kwafin muka mika ga hedikwatar zone, amma shiru har yanzu ba wani mataki, to wannan shi ya kai mu ga matakin da za a dauka a yanzu, na bayyana al’amarin ga ’yan jarida don jama’a su san halin da a ke ciki, ba wai saboda mu kanmu ba, saboda a cikin mun nan kowa ya fi karfin wannan kudi da muke magana a kai.
Ga kuma  sabuwar matsala da ta bayyana a yanzu, wadda ci gaba da kasancewarsa a matsayin shugaban jam’iyyar nan tamkar fifita yanki guda ne na Jihar Kebbi, a kan sauran yankuna biyu na jihar, kasancwarsa shi da Gwamna Atiku Bagudu da kuma Minista da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dauka a kwanan nan daga jihar, wato Barista Abubakar Malami, dukkansu sun fito ne daga yanki guda kuma gari guda, wato Birnin Kebbi.
Ba ma adawa da kasancewar gwamna ko minista a kan wadannan mukamai na su muna goyon bayan su, amma tun da haka ta kasance to a yi wa sauran yankunan Kebbi adalci, ta hanyar dako  shugaban jam’iyya daga daya daga cikin ragowar yankunanta biyu.

Aminiya: Bayan wata shida da nasarar da jam’iyyarku ta yi a matakin kasa da yawancin jihohi, sai ga shi an fara korafin rashin wanzuwar sauyi, ya al’amarin ya ke a jiharku ta Kebbi.
dan Maliki: Haka ne, sai dai ya kamata jama’a su yi dubi ga irin matsayi da a ka samu a yawancin jihohin, alal misali a jiharmu ta Kebbi ko kudin biyan albashi da jihar za ta biya bayan jam’iyyarmu ta karbi mulki ba a samu ba sai dai tarin bashi, da a ka ranto a banki, ga makarantu an gina da dama, amma babu malamai da za su tafiyar da su, kuma babu kayan aiki, ga tarin bashi na masu kwangilar ciyar da makarantu.
Haka dai gwamna ya kukuta  ya nemi tallafi ta bangarori daban-daban, har al’amarin ya yi kyau. Ya kuma inganta sha’anin wutar lantarki, saboda a baya ga wuta, amma ba wadatar turansfoma sai dai a rika rarraba wutar a tsakanin yankuna, ya kakkafa sababbin turansfoma a wurare daban-daban, shi ya sa yanzu a ke samun wuta a kodayaushe.

Aminiya: Babban abokin hamayyar gwamnanku, wato Janar Sarkin yaki Bello na jam’yyar PDP ya kai kararsa daga matakin karamin kotu har zuwa ta koli ba tare da nasara ba, yanzu ya shigar da wata karar a kotun yau da kullum, inda ya ke neman a kwace kujerar a bashi kan zargin a baya an taba kama gwamna Bagudu a kasar waje da laifin safarar kudi, ba ka jin wannan zai kai ga jami’yyarku ta rasa kujerar gwamna?
danmaliki: Ko kadan ba ma wannan fargaba, ai gabanin ya kai wannan karar a kwai wanda ya kai wannan maganar a baya, a lokacin da gwamna Bagudu ke matsayin sanata da ya nemi matsayin tare da shi, wani mai suna Sambo Aliyu daga jam’iyyar ACN, ba tare da ya yi nasara ba. Kai dai adawa ce kawai, kuma insha Allahu ba zai samu nasara ba.

Aminiya: A bangaren Shugaban kasa Buhari ma a kwai korafin cewa hada-hadar kudi a tsakanin al’umma ya yi rauni, ga layin mai, ga kuma ci gaban matsalar karancin wutar lantarki a wasu wurare.
danmaliki: Bai kamata jama’a su yi saurin mancewa da matsalar tsaaro ba, wadda ita ce babban dalili da a ka zabi shugaba Buhari a kai. Idan ka dubi wannan bangare sai Allah sam barka, ba don Allah ya amsa addu’ar bayinsa ba, da ba mu san halin da kasar nan za ta kasance ba izuwa yanzu, amma alhamdu lilLahi  kusan ya magance wannan matsalar in ban da ’yan burbudin hari  na lokaci zuwa lokaci.
Da ya rage wanda kuma a al’amari irin na ta’addancin magance daukacin matsalar a lokaci guda yana da wuya. Sannan ka da a mance da halin matsalar kudi da ya samu kasar nan a ciki, ga kuma karyewar farashin mai a kasuwar duniya.
Kuma Mataki da yake dauka na kafa jama’a ba na watsa musu kudi ba, kamar bangaren noma, wanda ya dau shirin farfado da shi kamar yadda ya kaddamar a kwanan nan a  Jihar Kebbi, ta hanyar tsara ba su horo, da rance  da kuma samar musu da kasuwa ga abin da suka noma, sauran jihohi za su biyo baya.