Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ce kara wa shugabannin Jam’iyyar APC wa’adi na shekara daya da aka yi a Fabrailu ya saba wa ka’ida.
Shugaban ya yi wannan jawabin ne a wajen taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar domin magance wasu matsalolin da suke fuskantar jam’iyyar wanda ke gudana a Hedkwatar jam’iyyar a Abuja.