✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bai dace FIFA ta rika tsoma baki a harkar shugabancin NFF ba -Alhaji Sani Fema

Shugaban hukumar wasanni ta Jihar Yobe Alhaji Sani Fema ya koka a kan yadda wadansu daga cikin shugabannin hukumar shirya kwallon kafa ta duniya FIFA…

Shugaban hukumar wasanni ta Jihar Yobe Alhaji Sani Fema ya koka a kan yadda wadansu daga cikin shugabannin hukumar shirya kwallon kafa ta duniya FIFA suka yawan tsoka baki a dambarwar shugabancin hukumar NFF ta Najeriya.
Alhaji Sani Fema wanda ya yi wannan kalami a lokacin da yake zantawa da wakilinmu a Damaturu ya bayyana takaicinsa na ganin yadda wadansu daga cikin shugabannin na FIFA suke neman jefa harkar kwallo a Najeriya a cikin mawuyacin hali a kokarin da suke yi na ganin an dakatar da Najeriya daga shiga harkar kwallo a kowane mataki a duniya saboda matsalar shugabancin da ya daibaibaye hukumar ta NFF.
“Ba mu ga dalilin da zai sa wasu jiga-jigan hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA su  rika tsoma baki da sunan hukumar ta FIFA ba alhali ba gaskiya ba ne,  dangane da al’amuran cikin gida na hukumomin kwallon kafa na kasashen duniya musamman danagane da dambarwar da ke tsakanin hukumar NFF ta kasar nan da kuma shugabanta Alhaji Aminu Maigari ba”. inji shi.
Alhaji Sani Fema wanda jigo ne a Hukumar NFF a wata karin magana da ya yi ya ce ai uwa tana dukan danta ne ba don ba ta son shi ba, sai dai don ta gyara masa hali don ya zama na kwarai a nan gaba, idan kuwa haka ne yakamata a ce Hukumar FIFA ta shigo al’amarin dambawar shugabancin Hukumar NFF ta Najeriya don don bayar da shawarwarin da suka dace don an gyara kurakuran da ake yi, ba wai a dauki matakin dakatar da Najeriya daga shiga harkar kwallo a kowane mataki a duniya ba.
 Ya kara da cewa  lallai akwai bukatar jiga-jigan na hukumar FIFA da ke shiga sharo ba shanu  su  shafa wa hukumar kwallon kafar  kasar nan NFF lafiya ta yadda hukumar za ta yi abin da ya dace ba wasu daga waje su rika tsoma baki ba.
 Da shugaban hukumar wasannin ya koma kan yadda hukumarsa a matakin Jihar Yobe ke samun tallafi daga gwamnati har ’yan wasan jahar na kwallon kafa da na kwallon gora (Hockey) suke samun nasara a gasar kasa da ake yi duk da matsalolin tsaro jihar ke fuskanta shugaban yabawa wa gwamnan Jihar a kokarin da yake yi na samar da kudaden tafiyar da harkar wasanni ba tare da gajiyawa ba.
Daga nan ya hori ’yan wasan jihar musamman na kungiyar Yobe Deseart da na kwallon gora da su ci gaba da nuna kwazonsu don ganin sun kai jihar ga nasara don ganin sun cigaba da daukaka martabar jihar a kasa da ma a idon duniya baki daya.