✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Badakalar Naira biliyan 2.5: An kama Dogarin Matar Shugaban kasa

Ana ci gaba da tsarewa tare da bincike kan Dogarin Uwargidan Shugaban kasa, Hajiya A’isha Buhari, CSP Sani Baba-Inna bisa zargin damfarar wadansu manyan mutane…

Ana ci gaba da tsarewa tare da bincike kan Dogarin Uwargidan Shugaban kasa, Hajiya A’isha Buhari, CSP Sani Baba-Inna bisa zargin damfarar wadansu manyan mutane ciki har da Sufeto Janar na ’Yan sandan Najeriya, Ibrahim Idris kamar yadda wata majiya a fadar Shugaban kasa ta sanar da Aminiya a ranar Talatar da ta gabata.

CSP Sani Baba-Inna, wanda ke tsaron A’isha Buhari tun shekarar 2016 yana ci gaba da fuskantar tambayoyi a ofishin jami’an taro tun ranar Juma’ar da ta gabata. Da farko ’yan sanda ne suka kama shi, daga bisani ya koma hannun DSS a Abuja.

Jaridar Premium Times da ke yanar gizo ce ta fara ruwaito labarin inda ta ce uwargidan Shugaba Buhari ce ta ba da umarnin a kame dogarin nata, bisa zargin yin sama da fadi da kudi har Naira biliyan 2 da rabi.

Wata majiya a fadar Shugaban kasa da ta bukaci a sakaya sunanta, ta ce an kama dogarin nata ne bisa yaudarar wadansu ’yan siyasa da sunan A’isha Buhari yana karbar kyaututtuka yana dannewa.

Majiyar ta kara da cewa ba Uwargidan Shugaban kasa ba ce ta ba da umarnin a kama shi.

“Ko alama ba Madam ce ta ba da umarnin kama dogarinta ba. Yana cutar mutane ne ciki kuwa har da Shugaban ’Yan sanda, Ibrahim Idris. Kuma ba a yi wa A’isha Buhari adalci ba idan aka ce ita yi umarnin a kama shi. Sai dai ba ta da ikon dakatar da binciken,” inji majiyar.

“Kuma maganar gaskiya ita ce CSP Baba-Inna ya jima yana yaudarar mutane. Bai damfari matar Shugaban kasa ba, don haka wannan ba damuwarta ba ce. Amma idan shugabanninsa suka gayyace shi don amsa tambayoyi kuma suka yi niyyar ladabtar da shi bisa rashin da’ar aiki, Madam ba za ta hana yin hakan ba,” inji majiyar.

Game da tambayar cewa ta yaya dogarin yake gudanar da ayyukan sai ya ce, “Kila yana ce musu Madam tana da wata gidauniya da take son kudaden tafiyarwa, su kuma mutane suke ba da gudumawarsu ga shirin, alhalin babu wani abu makamancin wannan.”

Da yake amsa tambayar yaya aka yi aka san kudin sun kai har Naira biliyan biyu da rabi sai majiyar ta ce Uwargidan Shugaban kasa ba ta wannan masaniya. “Abin da kawai aka sanar da ita shi ne dogarinta yana damfarar mutane da sunanta. Kuma a kan haka aka kama shi, sannan a kan haka ake bincikarsa,” inji shi.

A wata sanarwa da Kakakin A’isha Buhari, Suleiman Haruna ya fitar a ranar Talatar da ta gabata, ya  ce babu hannun matar Shugaban kasa a kan kama dogarinta.

To amma iyalan dogarin sun nuna takaicinsu kan lamarin, inda suka ce wannan kamu da bincike ba komai ba ne face wani yunkuri da wadansu ke yi don kau da Baban-Inna daga kan mukaminsa.