Majalisar Dattawa za ta tura tawaga ta musamman zuwa kasar Birtaniya kan tsare tsohon Mataimakin Shugaban Majalisar, Sanata Ike Ekweremadu, bisa zargin sayen sassan jikin dan Adam.
Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmad Lawan, shi ne ya sanar da hakan bayan wata ganawar sirri da Kwamitin Harkokin Kasashen Waje na Majalisar ya yi a ranar Laraba.
- Kotu ta ci dan sanda tarar N6m kan shiga gida babu izini
- ’Yan Bindiga sun kwace kauyuka 30 a Zamfara —Gumi
Sanata Ahmad Lawan ya ce tawagar, wadda za ta kunshi mambobin kwamitin za su bar Najeriya ranar Juma’a.
Ya ce za a tura tawagar ce bayan wata wasika da Ofishin Jakadancin Najeriya da ke Landan ya samu daga gwamnatin Birtiniya kan tsere Ekweremadu da matarsa, Beatrice.
Lawan ya bayyana cewa Ma’aikatar Harkokin Waje ta Najeriya da Ofishin Jakadancin Najeriya da ke Landon game da batun na Ekweremadu.
“Ofishin ya samu damar gudanar da ayyuka ciki har da ganawa da wasu lauyoyi da suka kare Ekweremadu kuma mun yaba mishi
“Mun yaba musu da abin da suka yi. Mun tattauna da Ministan Harkokin Cikin Gida kuma Ma’aikatar Harkokin Waje ta dauki matakan bayar da gudunmmawar da ta dace.
“Tunda abin na gaban kotu, abin da za mu iya yi dan kadan ne.
“Amma duk da haka ina tabbatar wa abokan arziki da iyalan Ike Ekweremadu da sauran ’yan Najeriya cea Majalisar Dattawa za ta tattauna da Ma’aikatar da ofishin jakadancin da ke Landan,” inji Sanata Ahmad Lawan.