Hukumar Yaki da cIN hanci da Rashawa (EFCC), ta saki dakataccen Akanta-Janar, Ahmed Idris.
A baya dai EFCC ta sami umarnin kotu a kan ta tsare Ahmed Idris na wasu kwanaki.
- Gobara ta tashi a gidan man AA Rano na Kano
- Shakira ta rabu da masoyinta Pique bayan kama shi da lalata da wata mata
Hukumar ta tsare Akanta-Janar din ne bisa zargin wawushe biliyan N80 daga baitil-malin gwamnati.
Aminiya ta jiyo cewa, EFCC ta saki Ahmed Idris din ne a ranar Alhamis bayan an ba da belinsa.
Tun bayan da Idris ya fada a komar EFCC dai gwamnati ta dakatar da shi daga mukaminsa na Akanta-Janar don gudanar da bincike.
Daga bisani kuma an sake gano wasu kudaden har kimanin Naira biliya 90 wadanda su ma ake zargin ya yi sama da fadi da su, jimlar Naira biliyan 170 ke nan.