Hukumar Yaki da Cin Hanci ta Kasa EFCC, ta gayyaci shugaban jam’iyyar PDP na Kasa, Uche Secondus da wasu shugabannin jam’iyyar, bisa zargin badakala da kudaden jam’iyyar.
Wannan na zuwa ne wata daya bayan wani jigo a PDP, Kazeem Afegbua, ya shigar da kara gaban EFCC, yana neman ta binciki shugaban Secondus da Kwamitin Tsare-tsaren Ayyuka kan karkatar da kudaden jam’iyyar.
- An yi garkuwa da alkali a cikin kotu
- Gwamnonin APC sun nemi El-Rufai ya sasanta da Kungiyar Kwadago
- ’Yar shekara 6 ta mutu sakamakon fyade a Kaduna
- Taron gwamnonin PDP bata lokaci ne —APC
Kazeem na zargi Secondus da yin ruf da ciki a kan kudaden jam’iyyar tare da yunkurin canja akalar jam’iyyar kafin zaben 2023.
Wasikar da EFCC ta aike wa Secondus a ranar 17 ga Mayu 2021, ta bukaci ya bayyana a ofishinta don kare kansa game da zargin da ake masa.
Kazalika ta bukaci ma’ajin jam’iyyar, sakatare da sauransu da su bayyana a ofishinta da ke Abuja, daga ranar 19 zuwa 21 ga watan Mayu, 2021.
Har wa yau, ta bukaci su zo da takardun bayanan kudaden fom din da ’yan takara suka saya tun daga shekarar 2017 zuwa yanzu.
Secondus dai ya musanta zargin kuma ya shigar da karar biliyan daya kan mai karar, Kazeem Afegbua.