Bayar da bashi ga magidanta masu neman karo aure na neman kawo yamutsi tsakanin ma’aurata a kasar Iraki.
Bankin Al-Rasheed na kasar ya fitar da tsarin bayar da rancen Dinare milyan (10), kimanin Dalar Amurka ($8,378) ga duk mijin da ke da son yi wa matarsa kishiya, wanda hakan ya jawo mata da dama a kasar yin bore.
- Kotu ta raba auren shekara 14 saboda zargin cin amana
- An raba auren shekara 18 saboda kaurace wa kwanciyar iyali
- ‘Ya kamata Sarkin Musulmi ya hana yin kayan aure’
- Taurin bashin kudin sadaki ya yi sanadiyyar mutuwar auren shekaru 32
“Bayar da bashi ga ma’aikata da bankin Al-Rasheed ke yi abun kunya kuma allawadai ne.
“Dalilin da bankin gwamnatin da ake gani da kima ya bayar na ba ma’aikatansa rance su yi wa matansu kishiya shi ne ma abin da ya fi ban kunya”, inji ‘yar siyasa a kasar Iraki, Hanan Al-Fatlawi.
Ta ce matakin da bankin ya dauka kaskantar da mata ne, inda ta ke cewa “mata ba kayan sayarwa ba ne”.
Rizan Sheikh Dlei, ‘yar Majalisar Dokokin Iraki, ta bukaci Firaminista Mustafa Al-Kadhimi da ya ba da umarnin soke rancen karo auren wanda ta ce na iya sa mata yin zanga-zanga.
Al-Fatlawi ta kara da cewa ya kamata gwamnatin kasar ta fito da sabbin tsare-tsaren da za su ba wa bankuna damar daukar mata aiki domin samun abin da za su dogara da kansu.