Wani dalibi mai suna Joseph Olona da ake yi wa lakabi da ‘Tort Angle’ da ke karatu a sashen Tsara Masana’antu a Jami’ar Kimiyya da Sana’a ta Tarayya (FUTA) da ke Akure ya rataye kansa.
Bayanai sun nuna dalibin ya dauki matakin ne saboda bacewar Naira dubu 100 mallakar sashen da ke hannunsa.
- Matsalar canjin kudi ce ta sa muka dakatar da ziyarar Buhari zuwa Kano – Ganduje
- Bayan zargin yi wa takararsa zagon kasa, Tinubu ya ziyarci Buhari a Daura
Aminiya ta jiyo cewa kafin rasuwar Joseph Olona shi ne Sakataren Kudi na sashen inda aka gano gawarsa a rataye cikin dakinsa na jami’ar a ranar Asabar da ta gabata.
Abokin marigayin mai suna Enoch Omoniyi ya ce matsalar ta faro ne a lokacin da Shugaban Sashen ya nemi marigayi Joseph Olona ya aika masa da kudin domin gudanar da wasu ayyukan sashen shi kuma Joseph ya aika da cakin kudin aka kasa fitar da kudin daga bankin.
Kuma tun daga lokacin da aka kasa cire kudin daga banki sai Joseph ya dakatar da halartar lacca bayan hutun Kirsimeti.
Shugaban kungiyar daliban Jami’ar FUTA, Jesufemi Asore ya tabbatar da aukuwar lamarin sai dai har zuwa lokacin rubuta wannan labari babu wani karin bayani a hukumance daga jami’an tsaro a Jihar Ondo.