Gwamnan Jihar Sokoto Aminu Tambuwal ya karyata rahotonnin ke cewa ‘yan bindiga na iko da wasu yankunan jiharsa.
Tambuwal ya bukaci masu yada labarin da su guji abin da zai saiyasantar da al’amarin tsaro ko zubar da kimar jami’an tsaro a jihar.
Ya kuma zargi ‘yan adawa da kitsa karyar don bata wa gwanatinsa suna.
“Muna maraba da suka mai ma’ana da bayanan da za su taimaka a magance wannan matsala.
“Amma ya kamata mutane su tabbatar da sahihancin abin da aka gaya musu kafin su yada”, inji shi.
- An girke jiragen da za su yaki ’yan bindiga a Sokoto
- ‘Yan bindiga: Gwamnonin Arewa za su yi taron dangi
- Jami’an tsaro sun kara matsa lamba kan ’yan bindiga a Sokoto
Wasu mutane da suka yi taron ‘yan jarida sun yi zargin cewa wasu yankunan jihar Sokoto na karkashin ikon ‘yan bindiga.
Sun kara da cewa sai da izinin ‘yan bindigar mazauna yankunan ke zuwa kasuwanni ko yin tarukan suna ko daurin aure.
“Da jin haka sai na nemi Darektan DSS da ya tambayi mashiryin taron a tsanake ya fada masa wuraren da abin ya shafa domin a ‘yanta mazauna.
“Amma da ya zo sai ya ce masa ingiza shi aka yi ya yi zargin sannan ya nemi afuwa”, inji Tambuwal.
Da yake jawabin yayin mika motocin sintiri guda 80 ga jami’an tsaro; Tambuwal ya jaddada aniyarsa ta kawo karshen matsalar tsaro a jihar.
Ya kuma bukaci jama’a su taimaka wa jami’an tsaro domin yakar mahara da sauran masu aikata manyan laifuka.
Gwamman ya ce jihar za ta bude cibiyar tara bayanan sirri na ko-ta-kwana daga jama’a da za a rika ba wa jami’an tsaro domin daukar matakin gaggawa.
Tambuwal ya kuma yi godiya ga Shugaba Buhari bisa yadda ya jajirce wajen magance matsalar tsaro a jihar Sokoto.