Hukumar Shirya Jarrabawar Kammala Sakandire ta Kasa (NECO), ta musanta zargin cewa akwai jarrabawar da ta tsara za a zana a ranar Babbar Sallah.
Hukumar ta ce an samu wasu na zarginta da sanya wata jarrabawarta a ranar bikin Babbar Sallah, wato 9 ga Yuli, lamarin da ta ce ba gaskiya ba.
NECO ta musanta hakan ne cikin wata sanarwa da ta fitar ta hannun Shugaban Sashenta na Yada Labarai da Hulda da Jama’a, Mista Azeez Sani, wadda aka raba wa manema labarai ranar Litinin a Abuja.
Jami’in ya ce, hukumar na sane da muhimmancin bukukuwan addini kuma tana kiyaye ranakunsu a duk lokacin da take tsara jadawalin zana jarrabawar.
Sani ya ce, “Babu wata jarrabawa da muka tsara za a rubuta har na tsawon mako guda, tun daga ranar 8 ga Yuli zuwa 13 ga Yuli.
“An yi hakan ne don bai wa Musulmai isasshen lokacin gudanar da bikin sallah,” inji shi.
Ana iya tuna cewa, a ranar 27 ga Yuni daliban da ke shirin barin makarantun sakandire a fadin kasar suka soma zana jarrabawar, wacce ake sa ran kammalawa a ranar 12 ga Agusta mai zuwa.
(NAN)