✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Babu wata Gwamnati a Najeriya —Jerry Gana

Mutane da dama sun kasa fahimtar cewa babu wata gwamnati a Najeriya.

Tsohon Ministan Labarai, Farfesa Jerry Gana, ya yi zargin cewa babu wata gwamnati a Najeriya.

Farfesa Gana ya bayyana hakan yayin da shi da wasu magoya bayansa suka sauya sheka zuwa jam’iyyar PDP a ranar Laraba.

A watan Maris na shekarar 2018 ne tsohon Ministan wanda ya kasance mamba a majalisar amintattu ta jam’iyyar PDP, ya sauya sheka zuwa jam’iyyar SDP (Social Democratic Party).

Yayin gabatar jawabansa ga mambobin jam’iyyar PDP a garin Bida na Jihar Neja inda aka yi liyafar dawowarsa jam’iyyar, Farfesa Gana ya ce Najeriya ta fada tsaka mai wuya kuma tana bukatar ceto na gaggawa.

A cewarsa, “Yanzu ba lokaci ne da za mu tsaya surutai ko yakin neman zabe ba, abin da kawai muke muradi shi ne mu taya juna farin ciki na dawowarmu wannan jam’iyya.”

“Za mu kasance tamkar tsintsiya madauri daya wajen gudanar da ingataccen aiki tare, sannan mu fita yakin zabe da karfinmu.”

“Ina mai tabbatar muku da cewa, za mu shimfida dabaru ta yadda za mu hambarar da wannan abu da ake kira gwamnatin jam’iyyar APC walau a jihar Neja, don babu wata gwamnati a jihar ballantana kuma a kasar baki daya.”

“Mutane da dama sun kasa fahimtar cewa babu wata gwamnati a Najeriya,” a cewar tsohon Ministan.

A bayan nan ne shugabannin jam’iyar PDP daga mazabun sanatoci uku na Jihar Neja, suka bai wa ’ya’yan jam’iyyar tabbacin za su ceto Jihar daga mummunan halin da ta tsinci kanta a hannun gwamnatin jam’iyyar APC.

%d bloggers like this: