Shugaban karamar hukumar Kajuru da ke jihar Kaduna, Mista Cafra Caino ya ce babu wani sabon hari da aka kai a dukkanin fadin karamar hukumar tun bayan 21 ga watan Mayun da ake ciki.
Shugaban ya kara da cewa majalisar karamar hukumar ta tashi haikan tare da hadin kan jama’ar yankin don tabbatar da zaman lafiya yayin da a lokaci guda kuma suke kokarin tallafa wa wadanda hare-haren baya suka shafa.
Shugaban, wanda ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a twitter a ranar Alhamis ya ce, ya samu tabbacin hakan ne daga masu rawunan gargajiya, inda ya ce a yanzu haka ana ci gaba da tuntuba tare da tattaunawa da juna don dawo da zaman lafiya a yankin.
“A yanzu haka jami’an tsaron da aka girke a dukkanin fadin karamar hukumar na ci gaba da kokari sannan gwamnati na bin diddigin lamarin ta hanyar amfani da rahotannin da take samu daga rundunonin sojan sama da na kasa da na ruwa da ke garin Kachia, da kuma jami’an tsaron DSS da kuma na ‘yan sanda.”
- An bude Gasar Rubutun Gajerun Labarai ta Aminiya-Trust
- ‘Dalilin bullo da Gasar Rubuta Gajerun Labarai ta Aminiya’
A karshe ya bayyana kokarin da gwamnan jihar, Mallam Nasir Ahmad El-Rufa’i ke yi ta hanyar gudanar da taro da shugabannin kabilun Adara da na Fulani da zababbun ‘yan siyasar yankin da kuma jami’an tsaro don nemo mafita kan yawan kashe-kashe da ramuwar gayya da ke aukuwa a tsakanin mutanen yankin.
Idan za a iya tunawa a kwanakin nan da ake ciki kashe-kashe ya dawo sabo a karamar hukumar da ke da tsohon tarihin fadace-fadace mai alaka da siyasa da addini da kabilanci da kuma rikicin manoma da makiyaya.
Hari na karshe da aka yi kafin rubuta wannan rahoto shi ne wanda aka kai wani kauye mai suna Gonan Rogo da ke karamar hukumar inda aka ruwaito an kashe mutum tara, yayin da kungiyar SOKAPU ta ce an kashe mutane kusa 27.
Tun daga lokacin ake ta musayan yawu tare da nunawa juna yatsa tsakanin kungiyoyin kabilar Adara da na SOKAPU a gefe daya, da kuma kungiyoyin Fulani makiyaya a daya gefen.