✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Babu wani aibu a sauya jam’iyya a siyasa —Kwankwaso

Kwankwaso ya ce da sauya sheka ake ganin irin farin jinin dan siyasa.

Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce bai ga wani aibu ba don dan siyasa ya sauya sheka zuwa wata jam’iyya, kasancewar hakan wani ginshiki ne na siyasa.

Tsohon gwamnan da ya mulki Kano sau biyu ya ce sauya sheka ga dan siyasa wata hanya ce da ke ba shi damar gane irin farin jininsa a siyasa.

Kwankwaso ya yi wannan furuci ne a Kano, lokacin da ya gana da jiga-jigan tafiyar Kwankwasiyya da kuma masu ruwa da tsaki na jam’iyyar PDP a gidansa da ke Miller Road.

“Zama a jam’iyya ko sauya sheka ba shi da aibu a siyasa. A takaice hakan zai sa mutum ya samu gogewa sannan ka san yadda za ka fuskanci kalubale,” a cewarsa.

Ya kuma bayyana yadda wadanda suka yi takarar a babban taron PDP na kasa a 2018, suka sun fice daga jam’iyyar sannan daga bisani suka sake komawa.

Kwankwaso ya ce har yanzu yana cikin PDP amma shirye-shirye sun yi nisa na sauya shekarsa zuwa jam’iyyar NNPP, tunda zamansa a jam’iyyar ya haifar da matsaloli da dama.

“APC babu abin da ta tsinana wa Najeriya, duk matakinsu daya da PDP. Duk yadda ka kai ga nagarta sai an samu wadanda za su yi kokarin kai ka kasa,” a cewarsa.

Idan ba a manta ba, a satin da ya gabata ne Aminiya ta kawo rahoton yadda Sanata Kwankwaso ya bayyana aniyarsa ta ficewa daga PDP, saboda yadda ya ce ake nuna mishi wariya: Sai dai wasu magoya bayansa sun ce ba za su bi shi zuwa NNPP ba.

Kazalika, ya bayyana yadda APC da PDP suka gaza yi wa Najeriya abun a-zo-a-gani, kuma ba su da wani abu da za su nuna da za a sake zabar su a 2023.