Kwamitin yakin neman zaben APC a Jihar Yobe ya musanta rahotannin da ke cewa an jefi gwamnan jihar, Mai Mala Buni a yakin neman zaben jam’iyyar a Karamar Hukumar Gashua.
Shugaban kwamitin, Sanata Muhammad Hassan ne ya bayyana hakan a taron manema labarai da ya gudanar a Damaturu ranar Lahadi.
- Gwamnatin Kano ta ba ’yan magani mako 2 su bar kasuwar Sabon Gari
- Kungiyar Musululmai ta nemi sauya lokacin kidaya saboda azumi
“Batun an jefi Gwamnan Buni kanzon kurege ne da wasu kafafen yada labarai ke yadawa.
“Ina sanar da ku cewa al’umma sun fito sun yi masa maraba, ba don su jefe shi ba.
Shi ma dai Babban Darkatan Yada Labaran Gwamnan, Mamman Muhammad ya ce wasu daga cikin magoya bayan APC din ne suka yi musayar yawu a tsakaninsu, amma babu wanin rikici da ya biyo baya.
“Abin da ya faru shi ne gwamnan ya hau mumbarin yin jawabi, sai dai yawan masoyan da ke kai ya sa ya fara kokarin karyewa.
“Wannan ne ya sa Babban Daraktan Yakin Neman Zaben APC, Sanata Muhammad Hassan ya dakatar da duk wani jawabi da za ayi, bayan na Shugaban Majalisar Dattijai Ahmad Lawan.
“Daga nan ne ya bai wa kowa umarnin ya sauka daga mumbarin don kar ya fado.
“Sai kuma wani sabani da aka samu tsakanin wasu mambobin yakin neman zabenmu, shi ma kuma babu fada, a lokacin kuwa Gwamnan da tawagarsa sun dade da barin wajen,” in ji shi.