Fitaccen malamin Musulunci, Sheikh Ahmad Gumi ya musanta labaran da ke cewa hukumar tsaro ta DSS ta gayyace shi domin amsa tambayoyi kan zargin sojoji da hada baki da ’yan bindiga.
Bayanin malamin ya zo ne awanni kadan bayan kakakin DSS, Peter Afunanya, ya tabbatar cewa hukumar ta gayyaci Sheikh Gumi, wanda ya ce ba bakon abu ba ne.
- An kama magidanci ya je kwartanci wurin matar amininsa
- Ana dab da fara cinikin filin jirgin saman Abuja, Kano da wasu guda 2
Wakilinmu ya tuntubi malamin da Magaribar ranar Juma’ar, inda ya shaida masa cewa, “Babu wanda ya gayyace ni, wasu kafafen yada labaran Kudu ne ke neman kawo rudani, amma da izinin Allah ba za su yi nasara ba. Mukan tattauna da shugabannin tsaro amma babu wanda ya gayyace ni.”
Sheikh Gumi, ya yi zargin ‘kafafen yada labaran Kudu’ sun kitsa labarin ne da nufin ganin an tsare shi.
Dambarwar gayyatar Sheikh Gumi
A safiyar Juma’a, mai magana da yawun Sheikh Gumi, wato Tukur Mamu, ya shaida wa Muryar Amurka (VOA) cewa hukumar DSS ta gayyaci Sheikh Gumi zuwa ofishinta da ke Kaduna.
Hakan ta sa aka alakanta gayyatar da wata hira da malamin ya yi da gidan talabijin na ARISE a ranar Laraba, wanda a ciki ya yi zargin hadin bakin tsakanin sojoji da ’yan bindiga.
A hirar, malamin ya ce babu yadda za a yi ’yan bindiga su rika samun makaman da suke amfani da su ba tare da hadin bakin baragurbin jami’an tsaro ba.
Tun gabanin dambarwar gayyatar, a ranar Alhamis, kakakin Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya, Birgediya Onyema Nwachukwu ya bukaci malamin ya sa wa bakinsa linzami.
Nwachukwu ya ce sojoji na sayar da rayukansu domin samar da tsaro, kuma duk da cewa suna maraba da suka mai ma’ana, ba za su lamunci duk wani yunkuri na goga wa jami’ansu kashin kaji ba.
Game da shiga daji yin da’awa ga ’yan bindiga, malamin, wanda tsohon hafsan soji ne, ya bayyana cewa kafin ya shiga daji inda yake ci gaba da ganawa dan ’yan bindiga, sai ya tattauna da hukumomin tsaro da sarakunan gargajiya da jami’an gwamnati kuma tare suke aiki.
Da aka tambaye shi game da rahoton DSS ta gayyace shi sai ya ce: “E, na karanta, sai abin ya ba ni dariya. Na ce a bar su su ji dadin abin da suke tunanin faduwata ce, amma karya ce, babu mahalukin da ya gayyace ni ba.”