✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Babu wanda na kullata a cikin wadanda suka yi takara da ni – Tinubu

Ya bayyana hakan ne a jawabinsa na lashe zabe

Dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, ya ce bai kullaci kowa daga cikin wadanda suka yi takara da shi a zaben fid-da gwanin APC ba.

Ya bayyana hakan ne lokacin da yake jawabi bayan ya lashe zaben fitar da gwanin jam’iyyar a filin Eagle Square da ke Abuja, inda ya ce kada su ji tsoron komai.

Aminiya ta rawaito cewa Tinubu ya lashe zaben ne bayan ya sami kuri’a 1,271 inda ya doke ragowar ’yan takara 13.

A cewar Tinubu, “Ina jinjina wa sauran ’yan takara. Takarar Shugaban Kasa akwai wahala sosai. Hakan ya kara wa jam’iyyarmu karfi sosai.

“Dole na mika gaisuwa ta musamman ga ’yan takara bakwai; Alhaji Badaru Abubakar da Sanata Ibikunle Amosun da Sanata Ajayi Borrofice da Dimeji Bankole da Godswill Akpabio da Kayode Fayemi da kuma Barista Uju Kennedy, wadanda suka ajiye bukatar kansu saboda hadin kai da nasarar jam’iyyarmu.

“Yanzu fadan ya kare. Wadanda ba su goyi bayana ba su daina jin tsoron komai, ban rike kowa ba a zuciyata.

“Ya kamata mu hada karfi da karfe mu yi aiki tare don ganin bayan PDP da magance matsalolin da suka hada da talauci da matsalar tsaro.

“Yanzu haka dai babban aikin da ke gabanmu shi ne na babban zabe a watan Fabrairun 2023. Mu yi kokari mu lashe zaben nan don mu kai kasarmu tudun mun tsira,” inji Tinubu.