✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Babu rigar mama ta zinare a kayan da aka kwace daga Diezani —Shugaban EFCC

EFCC ta ce babu wani abu mai kama da rigar mama ta zinare a kadarorin da ta kwace daga tsohuwar ministar

Hukumar Yaki da Masu Yi Wa Tattalin Arziki Ta’annati (EFCC) ta karyata cewa ta kwace rigar mama ta zinare daga tsohuwar Ministar Man Fetur, Diezani Alison Madueke.

Shugaban EFCC, Abdulrasheed Bawa, shi ne ya karyata labarin da aka yayata cewa akwai rigar mama ta zinare cikin kadadorin da hukumarsa ta kwace daga hannun tsohuwar ministar.

“Gaskiya babu wani abu mai kama da rigar mama ta gwal a kadarorin da muka kwace, shaci fadi ne dai na ’yan soshiyal midiya.

“Zan iya fada muku, ko ba ku tambaya ba, a matsayina na jagoran binciken, cewa ban san da rigar mamar da ake magan ba.

“Idan kuma har akwai ta, ya kamata dole in sani saboda ni ne jagoran binciken,” inji Bawa, kamar yadda ya shaida wa gidan talabijin na TVC a ranar Laraba.

Idan ba a manta ba a makonnin baya an yi ta yayata cewa Gwamnatin Tarayya ta yi gwanjon kadarorin da EFCC ta kwace daga hannun Diezani, ciki har da wata rigar mama da aka yi wa ado da zinare da lu’lu’, wadda darajarta ta kai Dala miliyan 12.3.

Labarin ya bulla ne bayan Gwamnatin Tarayya ta fitar da jerin wasu kadarorin da ta kwato daga hannun tsohuwar ministar, ciki har da wasu katafarun gidaje a yankin Banana Island da ke Jihar Legas.

A halin yanu dai Diezani, wadda ta bar Najeriya tun a shekarar 2015 tana kasar Birtaniya inda take fuskantar shari’a kan zargin ajiye kudi fiye da kima a gidanta da ke kasar.

Gwamnatin Tarayya na zargin ta da yin ruf da ciki a kan biliyoyin Naira a lokacin da take Ministar Albarkatun Man Fetur a lokacin gwamnatin Shugaban Kasa Goodluck Jonathan.

Tun a lokacin, an yi ta surutai a kan yadda ita da iyalanta ke rayuwar kasaita, wadda ake ta diga ayar tambaya a kai.