Gwamnatin Tarayya ta ce babu ranar bude makarantu a kasar ko da yake tana kan tattaunawa da masu ruwa da tsaki domin ganin an bude makarantun.
Minista a Ma’aikatar Ilimi Nwachukwu Nwajiuba yayin jawabi a taron Kwamitin Yaki da COVID-19 na kasa a Abuja ya bukaci manyan makarantu da ke gunagunin ci gaba da rufe su da su kara hakuri.
Ministan ya ce jami’o’i masu zaman kansu guda 78 sun bayyana wa Gwamnati cewa a shirye suke su ci gaba da darussa amma manyan makarantun gwamnati ba su cimma matsaya ba.
Ya bayyana fatar nan ba da jimawa ba za a samu sanar da ranar bude makarantun, amma ba sasakai ba.
Ya kara da cewa Ministan Ilimi, Adamu Adamu da kansa ya tattauna da masu ruwa da tsaki na manyan makarantu game da batun na sake bude su.
Nwajiuba ya ce bayan sauraron dukkanin bangarorin da abun ya shafa, zai tuntunbi kwamitin yaki da cutar na kasa domin yin nazari kafin a kai ga ayyana ranar bude makarantun.