✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Babu ranar daina amfani da tsoffin takardun Naira —CBN

CBN ya ce har kwanan gobe za a ci gaba amfani da tsoffin takardun Naira tare da sababbin da aka sauya wa fasali a Najeriya

Babban Bankin Najeriya CBN ya ƙaryata labarin da ke yawo cewa za a daina amfani da tsoffin takardun Naira 200 da Naira 500 da kuma Naira 1000.

CBN ya buƙaci ’yan Najeriya su yi watsi da rade-radin, wanda ya ce ba su da tushe.

Sanarwar da mai magana da yawun CBN, Hakama Sidi ta fitar ta ce har yanzu umarnin Kotun Ƙoli na ci gaba da amfani da tsofaffi da sabbin takardun Naira a tare nan yana aiki.

Ta ƙara da cewa har gobe CBN Bai janye umarni da ga bankuna da sauran cibiyoyin hadahadar kuɗaɗe na ci gaba da amfani da tsofaffin takardun kuɗin da aka sauya wa fasali ba.

A ranar Juma’a ne aka baza rade-radin cewa daga ranar 31 ga watan Disamba za a daina amfani da tsofaffin takardun kuɗi na Naira 200 da Naira 500 da kuma Naira 1,000 a koma amfani sababbin da aka sauya wa fasali.