Hukumar shirya kwallon kafa ta kasa (NFF) ta ce tuni ta kammala shirye-shiryen tafiyar gasar cin kofin duniya da za a yi a Brazil a  wannan shekara.
Hukumar ta ce tsoron da wasu ke yi na cewa da wuya ta iya samar da isasshen kudin da kungiyar Super Eagles za ta yi amfani da su a gasar ba gaskiya ba ne.  Hasalima tuni Hukumar ta gabatar da da adadin kudin da take bukata a kasafin kudin bana ga Gwamnatin Tarayya kuma ga dukkan alamu tuni gwamnatin ta amince da hakan.
A farkon watan da muke ciki ne dai Hukumar ta nemi  Kwamitin da ke kula da harkokin wasanni na Majalisar wakilai da ya tursasawa gwamnati wajen amincewa da bukatar hukumar don ganin an sakar wa Hukumar Naira biliyan biyu da ta nema don tafiya gasar cin kofin duniya a Brazil a watan Yuni mai zuwa. Sai dai wasu rahotanni sun nuna Gwamnatin Tarayya ta zaftare Naira miliyan 800 daga adadin Naira biliyan biyu da hukumar ke nema a kasafin kudin bana abin da ya sa aka rika tababar ko Hukumar ta yi shirin fuskantar gasar ba tare da an samu matsalar kudi ba.
Hukumar ta kiyasta za ta kashe akalla Naira biliyan biyu kwatankwacin Dala miliyan 11 ne a yayin gasar.
Haka kuma hukumar ta yanke shawarar cigaba da ba ’yan kwallon Super Eagles alawus din Dala dubu 10 kwatankwacin Naira miliyan daya da dubu 700 idan suka samu nasara a kowane wasa a zagayen farko.
Haka kuma Hukumar za ta ba ’yan kwallon alawus din Dala dubu 12 kwatankwacin Naira miliyan 2 da dubu 100 idan suka kai matakin zagaye na biyu yayin da ta ware musu Dala dubu 15 kwatankwacin Naira miliyan 2 da dubu 600 idan suka haye matakin kusa da na karshe watau Kwata-Fainal.
Shi kuma Koci Stephen Keshi an ware masa Dala dubu 20 kwatankwacin Naira miliyan 3 da dubu 400 a matsayin alawus idan kungiyar ta samu nasara a zagayen farko yayin da masu taimaka masa za su tashi da Dala dubu 15 kwatankwacin Naira miliyan biyu da dubu 600 idan kungiyar ta samu nasara a zagayen farko.
Babu matsala a shirye-shiryen tafiya gasar cin kofin duniya -Hukumar NFF
Hukumar shirya kwallon kafa ta kasa (NFF) ta ce tuni ta kammala shirye-shiryen tafiyar gasar cin kofin duniya da za a yi a Brazil a …