Wani gagarumin aikin da Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta himmatu akai tun bayan zuwanta kan karagar mulki yau kusan watanni tara, wanda kuma yake cikin alkawurran da ta xauka tun a lokacin yakin neman zabubbukan bara, shi ne yaki da cin hanci da rashawa, al`amarin da shi ne ummalhaba`ishin da ya daxe yana kassara rayuwa, tattalin arziki da zamantakewar al`ummar kasar nan. Wannan batu na yaki da cin hanci da rashawa da yanzu ya zama a kullum sai ka ji wani sabon labarin akan sa, dangane da irin yadda waxanda Allah Ya ba amanar dukiyar kasar nan da sunan shugabanci, musamman a cikin shekaru 16, da ake mulkin dimokuraxiyya ba kaukautawa, wato 1999 zuwa 2015, a inuwar jam`iyyar PDP, yanzu kuma ta ke bayyana irin waxancan shugabanni sun yi ta watanda da dukiyar al`umma, kamar yadda ake fallasa sunayensu, wasu ma sun gurfana gaban kuliya. Duk bayan binciken Hukumomi irin su Hukumar farin kaya ta SSS da ta yaki da ta`annati da kuxi jama`a, wato EFCC da kuma ta kula da xa`ar ma`aikata da kotunta wato ICPC da ta CCT.
Bincike da tonon sililin da ake kai yanzu a kan yadda ofishin tsohon mai bai wa shugaban kasa Kanar Sambo Dauki (mai ritaya) ya rinka raba kuxaxen sawo makamai don yakar `yan tada kayar baya, wato `yan kungiyar Ahlis Sunnah Lid-Da`awati Wal jihad da aka fi sa ni da Boko Haram, har Dala biliyan biyu da miliyan 100 ga wasu mutane na kusa da jam`iyyarsu ta PDP da na kusa da shi, da nufin ganin lallai sai tsohon Shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan ya ci gaba da mulki ko ta halin kaka a zaben 2015. Alhali a gefe xaya, mutanen kasar nan musamman na shiyyar Arewa maso Gabas suna ta fama da farmakin yaki `yan kungiyar ta Boko Haram ba dare da rana. Rikicin da sannu a hankali ya fantsama zuwa wasu jihohin kasar nan da ma na waxanda suke makwabtaka ta irin su jamhuriyar Nijar da ta Benin da Kamaru da Chadi.
Ana cikin wannan gagarumin yaki da irin waxancan mutane da suka isa a kasar nan, saboda irin xaukaka da darajar da Allah Ya yi musu, ya kuma ba su jagorancin al`umma a fannoni daban-daban a kasar nan, sai kuma aka ji Shugaban kasa Muhammadu Buhari yana faxa wa duniya cewa, wancan ta`annati na dukiyar jama`a kan sayo makamai da ake kai yanzu tamfar xigon ruwa ne ko xigon xanba a kan irin ta`annatin da aka yi da dukiyar al`ummar kasar nan, domin a faxarsa, har yanzu binciken bai kai kan Hukumomi irin na Kamfanin man fetur na kasa ba, wato NNPC da Hukumar tara kuxaxen shiga ta kasa wato FIRS da Hukumar hana fasa kwauri ta Kwastam, hukumomin da suke kan gaba cikin tara kuxin shigar kasar nan.
Mai karatu kar ka manta kafin, da ana cikin wannan fallasa ta waxanda suka sace kuxin kasar nan. Shugaba Buhari yana ta samun haxin kan shugabannin manya-manyan kasashen duniya irin nasu Nahiyar Turai da Amurka da Asiya da makamantansu da kungiyoyin duniya irin su Majalisar Xinkin Duniya UN da Bankin Duniya da Bankin bada lamuni na Duniya, wato IMF da kungiyar kasashe da suka fi karfin masana`antu a duniya da dai sauransu akan lallai za su mara masa baya akan wannan yaki na cin hanci da rashawa. Tabbaci na baya-bayannan da shugaba Buhari ya samu daga shugabannin irin waxannan kasashe, akan rufe kofa ga `yan kasar nan da suka saci kuxin kasar nan su kai waje, shi ne Shugaban kasar Haxaxxiyar Daular Larabawa wato UAE, Sheikh Muhammed Bin Zayad Al-Nahyan, mai Hedkwata a Dubai, Dubai xin da a `yan shekarunnan ta zama babbar cibiyar da shugabannin kasashe masu tasowa irin namu suke kai ajiyar kuxaxen da suka sata, bayan da tun a shekarun 1990, da kasashen Turai da Amurka suka rufe kofofinsu a kan shigar da haramtattun kuxaxe.
Dama dai a zaune take duk shugaban da ya xaura xamarar yaki da cin hanci da rashawa a kasashe irin kasr nan, to, lalle ya kwan da shirin cin hanci zai yake sa. Haka labarin yake yanzu a wannan kasa, tun bayan da Gwamnatin Shugaba Buhari ta mike gadan-gadan akan wannan mummunan alkaba`I da ya ke rusa rayuwar talakawa, ya raya ta wasu `yan kalilan.
Da farko `yan jam`iyyun adawa, musamman na jam`iyyar PDP, da ta rasa mulki a wannan karon sun ta zargin cewa akan `ya`yanta kawai yakin ya ke tsayawa, suna masu zargin an bar na sauran jam`iyyu, musamman `yan jam`iyyar APC mai mulki. Bayan sun ga wannan bai dakushe aniyar Gwamnatin Buharin ba, sai kuma suka rinka kiraye-kirayen sai binciken ya faro tun daga lokacin da kasar nan ta samu `yancin kai, ta yadda zai haxa da zamanin mulkin Shugaba Buhari na soja 1984 zuwa 1985. Ganin wannan bai karbu ba, sai kuma wasu suka bullo ta iyalen Shugaba Buhari inda suka yi zargin cewa Gwamnan Jihar Zamfara, Alhaji Abdulazez Yari yana neman xiyar Shugaba Buhari da aure, har ma ya bata kyautar Naira miliyan 40, zargin da gwamnan ya musanta.
Haka kwatsam, a ranar Alhamis xin makon jiya a lokacin da Mataimakin Shugaban kasa Mista Yemi Osinbajo yake karbar bakuncin ayarin Shugabannin kungiyar Musulmin Najeriya, wato MCN a karkashin jagorancin Imam Abdullahi Shu`aib, a fadar Aso Abuja, yana kokawa da cewa, Shugaba Buhari yana cikin tsananin matsin lambar wasu masu faxa a ji na kasar nan, a kan lallai sai Shugaba Buhari ya sassauta salon yaki da cin hanci da rashawar da ya xaura, har wai suna tunatar da shugaban kasar da cewa batun cin hanci da rashawa, ba wani sabon batu ba ne, da zai damu kansa da shi.
Mataimakin shugaban kasar dai bai faxi sunayen irin waxancan mutane masu kiraye-kirayen ba, amma ya ce sun fito daga sassa da kuma addinai daban-daban na kasar nan, wato Musulmi da Kirista. Ra`ayin irin waxancan mutane ne da mataimakin shugaban kasar ya ce a kullum suna tura wa shugaban kasa sakonnin neman ya sassauta xin, har suke ba shi shawarar idan har waxanda suka sace dukiyar kasar nan suka maido ta, to, kamata ya yi a kyale su, wato kar a hukuntasu.
Ka ji mai karatu, irin hujjojin rashin hujjar da irin waxancan mutane suke bayarwa, waxanda idan ka bi sawunsu za ka tarar ko dai suna cikin waxanda aka yi barnar da su, bincike ne bai zo kan su ba, ko kuma sun mori wani abu daga cikin barnar da aka yi. Amma abin tambaya shi ne, haka za mu yi ta zama mutane na sace kuxaxen da za a yi wa al`ummar kasa aiki, su je su kai su inda su ba su amfana ba, na tare da su ma ba su amfana ba? Mun yi wani lissafi da wasu abokan aiki a kwanannan a kan wanda ya saci =N=1biliyan, sai ya kwashe shekaru 100, a kullum yana kashe =N=25,000, kana kuxi za su kare.
Ina ga babu wani dalili da zai sanya Shugaba Buhari ya saurari kiraye-kirayen irin waxancan mutane, saboda yaki da cin hancin da yake na cikin alkawurrun da ya yi wa masu zabe a cikin yakin neman zabensa, kuma talakawan kasa suna maraba da shi. Haka za mu yi ta zama wasu mutane `yan kalilan na yin abin da suka ga dama suna kwana lafiya, talakawa na cikin wahala. Babu wani sabo a kiraye-kirayen irin waxancan mutane. Allah Ya kama.
Babu mamakin yunkurin neman hana yakar cin hanci da rashawa
Wani gagarumin aikin da Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta himmatu akai tun bayan zuwanta kan karagar mulki yau kusan watanni tara, wanda kuma yake cikin…