Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya dauki alwashin dakile rashawa a harkar kashe kudaden kamfen a kasar, kuma ba zai amince da amfani da wasu kudaden gwamnatin wajen sake zabensa a karo na biyu ba.
Shugaban ya bayyana hakan ne yayin taron majalisar zartarwa da aka saba yi duk mako, shugaba Buhari ya bukaci ministocin kasar su yi amfani da wannan damar wajen wayar da kan masu kada kuri’a akan sake zaben jam’iyyar APC a babban zabe na watan gobe.