✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Babu kasar da za ta gwada mana yadda za mu yi da kasar Syria – Ministan Tsaron Isra’ila

Ministan Tsaron kasar Isra’ila, Abigdor Lieberman ya ce kasarsa ba za ta amince da takura na ko kuma wata kasa ta tilasta mata wajen zagaitawa…

Ministan Tsaron kasar Isra’ila, Abigdor Lieberman ya ce kasarsa ba za ta amince da takura na ko kuma wata kasa ta tilasta mata wajen zagaitawa ga kasar Syria.

Ministan ya yi wannan jawabin ne bayan an ambaci sunan kasar Isra’ila a cikin wadanda ake zargi da wani mummunan hari da aka kai makon da ya gabata.

“Babu ruwanmu da kowa, kuma za mu ci gaba cin gashin kanmu ne a wannan lamarin. Babu wata kasar da za ta fada mana yadda za mu yi musaman a bangaren kare kasarmu da muradun ’yan kasar,” inji Lieberman a wani faifan bidiyo da yake amsa tambayoyin manema labarai daga kafar yada labarai ta Walla a kan yadda kasar Rasha ke nuna musu dan yatsa a kan harin da aka kai a Syria. 

Ministan Tsaron ya kara da cewa ba wai suna da nufin bata wa kasar Rasha rai bane ko kuma su shigar das u cikin maganarsu, “Ba mu da burin bata wa mutanen kasar Rasha rai. Muna da tsarin yadda muke isar da sako mai muhimmanci a matsayin manyan hafsosi. Mutanen kasar Rasha sun sanmu, sannan kuma maganar gaskiya ita ce mun dade muna kokarin kaucewa duk wata baraka da ka iya kunno kai tsakaninmu da su, kuma suna da masaniya a kan hakan musamman a game da rikicin kasar Syria,” inji shi. 

Sannan kuma Lieberman ya zargi manyan makiya kasar Isra’ila da kokarin fadada shirinsu tare da mallakar sansanonin soji a kasar Syria, wanda hakan ba karamin barazana bane ga kasarsa.

A cewarsa, “Ba za mu amince da tsarin ajiye sojojin Iran ba a kasar Syria da sunan sojojin tashar jirgin ruwa ko kuma sojojin tashar jirgin sama da kuma ajiye makamai masu linzami da wayau,” inji shi.

A ranar 9 ga watan Afrilun bana, an kashe mutum 14 ciki har da sojojin Iran guda 7 a wani hari da aka kai sansanin T=4 da ke kasar Syria, inda kasashen masu hamayyya na Isra’ila da Rasha suka zargi kasar Isra’ila da kai harin. 

Daga bisani sai Shugaban kasar Rasha bladimir Putin ya kira Firayi Minsitan kasar Isra’ila Benjamin Natanyahu da cewa kada ya dauki wani mataki da zai iya kawo kara tabarbarewar al’amura a kasar Syria.

Har yanzu dai kasar Isra’ila bat a karyata ba kuma bat a tabbatar da ko ita ta kai harin ba