✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Babu kasar da ba a ba da tallafi —Falana

Falana, ya ce yaki da masu fasa bututun mai shi ne abin da ya kamaci Twamnatin Tarayya.

A yayin da ake ci gaba da fuskantar karancin man fetur a sassan kasar nan, lauya mai kare hakkin dan Adam, Femi Falana, ya nuna adawarsa ga shirin Gwamnatin Tarayya na cire tallafin man a watan Yunin 2023.

Falana ya ce ko kadan ba ya goyon bayan cire tallafin mai, domin a cewarsa, babu wata kasa a duniya da ba ta tallafa wa jama’arta don su ji dadi.

Ya bayyana a wata tattaunawa da gidan talabijin na Channels ya yi da shi cewa “Ba zan taba goyon bayan cire tallafin man fetur ba.

“Dalili shi ne sashe na 14 na kundin tsarin mulkin kasar nan ya tanadi cewa tsaro da jin dadin jama’a su ne babbar manufar gwamnati.

“Don haka dole ne gwamnati ta kula da irin halin da jama’a  za su shiga a sanadin cire tallafin,” cewar Falana.

Lauyan ya koka kan gazawar Gwamnatin Tarayya wajen hako gangar danyen mai miliyan 1.8 a kowace rana sakamakon fasa bututun man da barayi ke yi.

“Dalilin da aka zabe ku a matsayin gwamnati shi ne don yakar masu aikata laifukan da za su shafi tattalin arziki da sauransu.

“Amma wadannan su ne abubuwan da ke faruwa a kasarmu,” inji shi.

Dangane da yadda za a kawo gyara kan batun cire tallafin man, Falana ya ce Majalisar Dattawa ta gaza gudanar da aikinta yadda ya dace shi ya sa gwamnati ke kokarin asassa cire tallafin.

A baya-bayan nan Gwamnatin Tarayya ta sanar da cewa za ta cire tallafin man fetur duba yadda take tafka asara a sanadiyyar bayar da tallafin.

A wani bangaren kuma, gwamnatin na fama da masu fasa bututun mai wanda a sanadin haka makudan kudade suke zurarewa, sannan ba a samun adadin danyem man da ya kamata a fitar a kullum.