Sarkin Hausawan Jihar Imo, Alhaji Auwal Baba Sa’idu Sulaiman, ya karyata labarin da wasu ke yadawa a kafofin sada zumunta cewa mahukunta a Jihar sun kori wasu ‘yan Arewa daga matsugunansu.
Rahotanni dai sun ce an kori mutanen ne a natsugunansu da ke unguwar Avu-Junction da ke birnin Owerri, babban birnin Jihar.
- Abin da ya hana ni zuwa taron da aka tabbatar da Ganduje a Shugabancin APC — Buhari
- Yanzu-Yanzu: Ganduje ya zama shugaban APC
Sarkin Hausawan ya karyata labarin ne cikin hirarsa da Aminiya ta wayar salula, inda ya ja kunnen irin wadannan mutane cewa, “Ku gujewa yada labaran karya da za su iya haddasa kyamar juna da rikici a tsakanin al’ummar kasa.
“Wannan unguwa ta Avu-Junction a garin Owerri wuri ne da ya hada kabilun kasa daban-daban da suke zaune a ciki. Hausawan da ke zaune a wannan wuri ba su wuce kaso 30 na yawan sauran kabilu ba. Kuma wuri ne da yayi kaurin suna ta fannin kasancewa maboyar makamai da ’yan fashi ke amfani da su wajen aikata miyagun ayyuka.
“Shi ne dalilin da ya sa Gwamnatin Jihar daukar matakin tura jami’an tsaro su kama tare da fatattakar dukkan wadanda ake zargi da aikata miyagun ayyuka a wannan wuri.
“Jami’an tsaro sun je Avu-Junction ne bayan samun labarin irin makaman da aka boye a wurin da wasu mutane biyu da aka yi garkuwa da su da jami’an suka yi nasarar kubutar da su tare da kama masu aikata miyagun ayyuka.
“Jami’an tsaron basu je wannan wuri domin musgunawa Hausawa ko kama su ba. Sun je a kan aikinsu na tsaro ne. Wannan ne gaskiyar abun da ya auku a Unguwar Avu-Junction ba kamar yadda wadannan mutane suka tsere zuwa Arewacin kasa suna bayar da labaran karya ba,” inji Sarkin Hausawan na Imo.
Alhaji Awal Baba Sa’idu Sulaiman ya ce, “A binciken da muka gudanar a cikin unguwar Avu-Junction, mun gano cewa akwai wasu ‘yan Arewa da suke safarar kananan yara maza da mata daga Jihohin Arewa zuwa wannan wuri da suke amfani da su wajen samun kudi ta hanyar koya masu shaye-shayen kwayoyi da aikata miyagun ayyuka da karuwanci da suke bata mana suna.”