✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Babu inda aka dasa bom a Abuja —Rundunar ‘Yan sanda

Rundunar ’yan sandan Babban Birnin Tarayya Abuja ta karyata rade-radin da ake yadawa na cewa an dasa bama-bamai a birnin. Bayanin haka ya fito ne…

Rundunar ’yan sandan Babban Birnin Tarayya Abuja ta karyata rade-radin da ake yadawa na cewa an dasa bama-bamai a birnin.

Bayanin haka ya fito ne ta sanarwar da kakakin rundunar, Oluyiwa Adejobi ya fitar yana gargdin jama’a da su kiyayi yada jita-jita maras tushe ballantana makama.

“Muna masu kara jaddada cewa yankin babban birnin tarayya na cikin zaman aminci, kuma babu wata barazana ga lafiya ko dukiyar kowa,” in ji Kakakin.

Sannan ya yi kira ga jama’ar da ke ciki da kuma wajen yankin da su yi watsi da wannan labari na karya da ake yadawa don kawai a firgita jama’a.

Ya kuma ce, rundunar ’yan sandan na ci gaba da daukar matakan tsaron da suka kamata an kawar da duk wasu ayyuka na bata gari a kasa baki daya.

Hankulan jama’a a Najeriya ya tashi matuka tun makon da ya wuce sakamakon sanarwar da Amurka ta fitar na cewa za a kai wa babban birnin harin ta’addanci.

Ofisoshin jakadancin kasashe da ke birnin sun gargadi ’yan kasarsu kan sanarwar ta Amurka, tare da umarnin su da kiyaye.

Shugaba Buhari ya kwantar wa ’yan kasa hankali kan lamarin, yana cewa jami’an tsaro na aikinsu yadda ya kamata don kawar da duka wata barazana ga birnin da ma kasa baki daya.