✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Babu imani ga mai cutar da makwabcinsa (2)

Huduba ta Biyu: Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai. Tsira da amincin Allah su kara tabbata a bisa mafificin manzanni da alayensa da sahabbansa…

Huduba ta Biyu:

Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai. Tsira da amincin Allah su kara tabbata a bisa mafificin manzanni da alayensa da sahabbansa baki daya.
Bayan haka, ya ku Musulmi! Lallai Musulunci ya wajabta taimakon juna da kyautatawa a tsakanin mutane, kuma ya haramta cuta da ta’addanci. Ya tsayar da alaka a tsakanin halittu bisa soyayya da ’yan uwantaka da tausayawa da cika alkawari. Saboda haka ne Musulunci ya yi wasiyya kan makwabci, ya yi umarni da kyautata masa, ya karfafa hakkinsa, ya tsoratar kan cutar da shi. Manzon Allah (SAW) ya ce: “Jibrilu bai gushe ba yana yi min wasiyya da makwabci har na zaci cewa zai gaje shi.” Don haka kyautata wa makwabci yana daga cikin alamun Imani, cutar da shi kuma yana kore wannan Imani daga mutum. Mai tsira da amincin Allah ya ce: “Ka kyautata wa makwabcinka, sai ka kasance mumini, kuma ka so wa mutane abin da kake so wa kanka, sai kasance Musulmi.” Kuma ya ce: “Wallahi ba ya da imani! Wallahi ba ya da imani! Wallahi ba ya da imani!” Aka ce, “Ya Manzon Allah ya tabe kuma ya yi asara, wane ne wannan?” Ya ce: “Wanda makwabcinsa bai kubuta daga sharrinsa ba.” A cikin wannan akwai girmama sha’anin hakkin mawabci da tsoratarwa kan cutar da shi da musguna masa.
Ya ku muminai! Lallai kyautata wa makwabci yana kasancewa ne ta hanyar ba shi hakkinsa da kamewa daga cutar da shi, kuma kokartawa don taimakonsa na daga cikin hakkin makwabci a kanka. Kuma ka yin masa sallama idan ka hadu da shi, ka karbe shi da sakakkiyar fuska da fara’a, kuma ka taimake shi idan ya kasance fakiri. Ka je gaishe shi idan bai da lafiya, ka tallafa masa idan ya kasance mabukaci. Ka kawar da kai daga gazawarsa ka kare mutuncinsa ka boye sirrinsa. Manzon Allah (SAW) ya ce: “Wanda ya taimakin dan uwansa a boye, Allah zai taimake shi a duniya da Lahira.” Baihaki ya ruwaito.
Abin da ake nufi da cutarwa shi ne a guji nuna alfahari da isa a kan makwabci ko munanta zato gare shi, ko yi masa leken asiri, ko gibarsa, ko yin wani abu na isar da cutarwa ko sharri gare shi. Ko ka yi wani abu da zai jawo wa makwabcinka matsala wajen jin dadin rayuwarsa ko kuntata masa, ko kasance mai yi masa kulli ko hassada kan wata ni’ima da Allah Ya yi masa. “Muna neman tsarin Allah daga sharrin mai hassada idan ya yi hasada.”
Yana daga cikin wauta da raunin tunani mutane su rika kai kara kan abin da ya shafi makwabta na daga husumar mata da fadace-fadacen yara. Kuma daga cikin abin da ya zo daga Manzon Allah (SAW) akwai hanin da ya yi kan tsawaita gini idan ya zamo hakan zai cutar kamar kange iska da nuna isa ga wanda yake zaune tare da kai. Hakika Manzon Allah (SAW) yana cewa: “Ya Allah! Ina nema tsarinKa daga mugun makwabci a gidan zama, domin makwabcin daji yana sauyawa.” Kuma (SAW) ya ce: Ya Allah! Ina neman tsarinKa daga aboki mai makirci, idanuwansa na kallona, zuciyarsa taba kiwona. Idan ya ga abu mai kyau ya turbude shi, idan ya ga abu mummuna ya watsa shi.” Buhari ya ruwaito. Kuma (SAW) ya ce: “Ka guji abubuwan da aka haramta, sai ka kasance mafi ibadar mutane. Ka yarda da abin da Allah Ya ba ka, sai ka kasance mafi wadatar mutane. Ka kyautata wa makabcinka don ka kasance mumini, ka so wa mutane abin da kake so wa kanka, sai ka kasance Musulmi. Kuma kada ka yawaita dariya domin yawan dariya yana kashe zuciya.”
Wani ba ruwansa da kowa idan shi yana jin dadi, ba ya damuwa idan dukkan bayin Allah za su fadi a kansa su bata shimfidarsa matukar dai zai samu biyan bukata ya cimma burinsa ya biya sha’awarsa, halinsa ya kyautata, koda hakan zai jawo halakar wani, ko shi ya barin addininsa ya sanya ya rasa girma da martaba. Saboda haka sai ka gan shi abin ki a tsakanin ’yan uwansa, abin kyama a tsakanin makwabtansa, marashin nauyi a mizaninsa. Daga cikin abubuwan da mutane suka riska na maganganun annabawan farko akwai: “Idan b aka ji kunya, to ka aikata abin da ka so.” Kuma     Manzon Allah (SAW) ya ce: “Lallai Allah Ya rarraba muku dabi’unku a tsakaninku, kamar yadda Ya rarraba arzikinku a tsakaninku. Kuma lallai Allah Yana bayar da duniya ga wanda Yake so da wanda ba Ya so, amma bai bayar da addini sai ga wanda Yake so. Duk wanda Ya ba shi addni hakika Ya so shi. Kuma na rantse da Wanda raina ke hannunSa, bawa bai kubuta har sai zuciyarsa da harshensa dun zamo kubutattu, kuma bai zama mumini har sai nakwabcinsa ya kubuta daga sharrinsa.”
Godiya ta tabbata ga Allah a farko da karshe. Ya Allah Ka kara tsira da aminci a bisa Muhammad da alayensa da sahabbansa. Allah Ya sanya ni da ku a cikin mafi alherin halittunSa, kuma Ya yi mini da ku albarka da tsarkakan abubuwa na daga arzikinSa. Ya tsirar da ni da ku daga cutar da makwabci da wasa da hakkinsa, amin.
“Ku bauta wa Allah, kada ku yi shirki da Shi, game da mahaifa biyu ku kyautata, kuma kun kyautata wa makusanta da marayu da matalauta da makwabci makusanci da makwabci na gefe da abokin tafiya da dan tafarki da kuma abin da damarku ta mallaka. Lallai ne Allah ba Ya son wanda ya kasance mai girman kai mai alfahari.”
Allah Ya yi min albarka da ku a cikin Alkur’ani Mai girma, kuma Ya amfanar da ni da ku da abin da ke cikinsa na ayoyi da zikiri mai hikima. Ina fadin wannan magana tawa, ina mai neman gafarar Allah Mai girma gare ni da ku da sauran Musulmi daga dukkan zunubi. Ku nemi gafararSa lallai ne Shi Mai gafara ne Mai jinkai.
Subhana rabbika rabbil izzati amma yasifun. Wa salamun alal mursalin. Wal hamdu lillahi rabbil alamin.