✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Babu hikima a hana ‘yan Najeriya shiga Birtaniya —Lai Mohammed

Ministan ya ce babu adalci da hikima ga hana 'yan Najeriya shiga Birtaniya

Gwamnatin Tarayya ta yi kira ga gwamnatin Birtaniya da ta janye takunkumin shigar kasarta da ta sanya wa ’yan Najeriya saboda samun kwayar nau’in Omicron na COVID-19 a Najeriya.

Ministan Yada Labarai da Raya Al’adu, Lai Mohammed ne, ya yi wannan kira yayin ganawa da manema labarai a Abuja, a ranar Litinin.

Lai Mohammed, ya ce sam babu hikima a cikin matakin da gwamnatin Birtaniya ta dauka, kuma akwai rashin adalci game da matakin.

Ya ce duk da cewa kwamatin yaki da COVID-19 a Najeriya zai dauki matakin da ya dace, “Ni a matsayina na mai magana da yawun gwamnati ina kallon matakin a matsayin zalunci”, kuma Birtaniya ba ta zartar da hukuncin ta hanyar da ta dace ba.

Har wa yau, ya bayyana mamakinsa kan yadda za a dauki matakin kan kasa kamar Najeriya wadda ke da al’umma fiye da miliyan 200, saboda wasu mutane kalilan sun kamu da nau’in kwayar cutar.

Sai dai tun bayan sanar da matakin a kan Najeriya, Ofishin Jakadancin Birtaniya a Najeriya ya dakatar da bayar da bizar shiga kasar ga ’yan Najeriya.

Har wa yau, kamfanin zirga-zirgar jirage na ‘British Airways’ ya dakatar da sayar da tikitinsa ga ’yan Najeriya.

Tuni mutane da dama da suke shirin shiga Birtaniya suka fara kokawa kan matakin da gwamnatin ta dauka, wanda bai yi wa mutane da dama dadi ba.