✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ganduje ya dakatar da hawan Babbar Sallah a Kano

Babu ziyara zuwa gidan Shettima, Hawan Daushe, Hawan Nassarawa da sauransu.

Gwamnatin jihar Kano ta sanar da soke dukkannin bukukuwan hawan Babbar Sallar da aka saba yi bana.

Gwamnatin ta ce daukar matakin ya zama wajibi don ganin nasarar da jihar ta samu a wajen yaki da annobar COVID-19 ta dore.

Kwamishinan Yada Labarai na Jihar, Muhammad Garba ya sanar da ‘yan jarida ranar Laraba ewa Majalisar Zartarwar jihar ce ta yanke shawarar daukar matakin yayin zamanta na ranar Talata.

Ya ce, “Ko da yake za a kyale al’ummar jihar su gudanar da sallar idi kamar yadda aka saba, gwamnati za ta dauki matakan da suka dace wajen ganin an bi dukkan ka’idojin kariya a masallatan”.

Kwamishinan ya ce dukkan sarakunan yanka na jihar guda biyar za su gudanar da sallar ne a garuruwansu, kuma ba za a gudanar da ziyara zuwa gidan Shettima, Hawan Daushe, Hawan Nassarawa da sauran bukukuwan al’ada da masarautun suka saba gudanarwa ba.

Muhammad Garba ya kuma ce gwamnatin jihar za ta tallafa wajen samar da kayan kariya kamar su takunkumi, sunadaran tsaftace hannu da kuma bayar da tazara.

Idan dai za a iya tunawa, ko da Karamar Sallah bana ma ba a gudanar da bukukuwan ba saboda annobar ta COVID-19.