Shugaban Kungiyar Fulani Makiyaya ta Miyetti-Allah ta Najeriya reshen jihar Binuwai, Risku Mohammed ya musanta zargin da ake yi cewa Fulani ne suka kai wa ayarin Gwamnan jihar, Samuel Ortom hari.
A ranar Asabar ne dai aka kai wa Gwamnan hari a kusa da gundumar Tyomu lokacin da yake kan hanyarsa ta dawowa daga Gboko zuwa Makurdi da tsakar rana.
- Na yi nadamar goyon bayan Buhari a 2015 – Dino Melaye
- Buhari ya amince a fara biyan sabbin ma’aikata 774,000 albashi
Risku Mohammed a wata tattaunawa ta wayar salula ya shaidawa wakilinmu cewa ya yi tafiya zuwa jihar Nasarawa kuma ba shi ma da masaniya a kan harin.
“Idan Gwamnan ya ce an kai masa harin ne a kan hanyarsa ta zuwa gona to ta yaya Fulani za su kai mishi harin? Ta yaya suka san inda ma za shi? Babu hannun Fulani a ciki,” inji shugaban.
A baya dai Gwamna Ortom ya sha zargin kungiyar ta Miyetti-Allah da kitsa makamantan wadannan hare-haren ko da yake sun sha musanta hakan.