Tsohon Gwamnan Jihar Legas kuma dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu, ya ce babu wani Gwamna a tarihin Najeirya da ya fuskanci bincike kamar shi.
Ya ce duk da binciken na kwa-kwaf da aka yi masa babu abin da aka samu.
- DAGA LARABA: Jabun Kayayyaki: Ina Hukumar SON Ta Shiga Ne?
- ’Yan bindiga sun sace wasu mata a kantin magani
Tinubu ya bayyana hakan ne ranar Talata a tattaunawarsu da kafar BBC yayin ziyarar da ya kai London.
Dan takarar ya kuma bayyana ce-ce-ku-cen da ake yi game da dukiyarsa a matsayin hassada da kyashi.
Tinubu ya kuma ce a duk cikin ‘yan takarar Shugaban Kasa shi ne ya fi cancanta ya shugabanci Najeriya a zaben 2023 mai zuwa.
Ya kara da cewa, yana da yakinin muddin aka gudanar da sahihin zabe a 2023, shi ne zai lashe shi.
Tsohon Gwamnan ya ce, fannin tsaro da tattalin arziki su ne fannonin da zai bai wa muhimmanci muddin aka zabe shi Shugaban Kasa.